An bukaci membobin kungiyar Yan kasuwar Arewacin Najeriya da sukasance masu hada kansu.

Biyo bayan ta kaddaman shugabanci da ya kunno kai a cikin shugabanci kungiyar yan kaauwar arewacin Najeriya wato Arewa Traders Association a Nigeria, ATAN a matakin kasa hakan yasa shuwagabanin kungiyar a matakin jihohi ke nuna goyon bayansu ga shugaban kungiyar na kasa Alhaji Muhammed Ibrahim 86 wanda a cewarsu su suka sani a matsayin zababben shugaban kungiyar ta kasa kamar yadda dokan kungiyar ya tanada. Shugaban kungiyar yan kasuwa a arewacin Najeriya shiyar jahar Kogi Dr Umar Muhammed ne ya baiyana haka a zantawarsa da manema labarai dangane da matsalolin rarrabuwar kai da ake samu a kungiyar. Dr Umar Muhammed yace suma suna zaune ne kwatsam sai sukaji wai ga wasu da aka baiyanasu a matsayin shuwagabanin kungiyar Arewa Traders Association of Nigeria wanda kuma basu San da suba domin kuwa ba abi dokan kungiyarba asalima wannan shine ake kira sojan gona, ko kuma shigan biltu. kuma abin manakinma shine wanda yake ikitarin cewa shine shugaban kungiyar yan kasuwa na arewacin Najeriya shinefa bayan an gudanar zaben Alhaji Myhammed Ibrahim 86 a matsayin shugaban kungiyar ya bada goyon baya wanda yabi shugaban har yola domin tayashi murna saboda haka bai kamata a yanzu kuma yace shine shugaban kungiyarba don kuwa bazabansa akayiba. Don haka Alhaji Muhammed Ibrahim 86 shine halaceccen shugaban kungiyar ta kasa saboda an bi dukkanin ka idodin wajen gudanar da zabensa, wanda ya samu amincewar dukkanin shuwagabanin jihohi da sakatarorinsu saboda haka ba wani dalilin da zaisa wasu haka kawai su aiyana Kansu a matsayin shuwagabanin da doka baisan dasuba harma suna ikirarin rusa kwamitin amintattun kungiyar, wannan ba daidaibanne. Dr Umar yace abinda ya bashi mamakima shine a lokacinda aka zabe Alhaji Muhammed Ibrahim 86 a matsayin shugaban kungiyar sun Nina goyon bayansu da wannan zabe, to in ba son zuciyaba da son mulkiba ya kamata su hakura har wa adin zababen shugaba ya kare in suna bukata sai su shiga zabe, wanda Allah ya baiwa nasara while nen sai yayi shugabanci. A Cesar Dr Umar wasu daga cikin masu ikirarin sune shuwagabanin kungiyar basu da katin shaidar membibin kungiyar, don haka ya kamata suyiwa kansu kiyamul laili suzo a hada kai domin ganin kungiyar ta cigaba yadda ya kamata wanda hakan zai kawo cigaban kungiyar dama yankin na arewacin Najeriya baki daya. Da wannan ne Dr Umar ya kirayi masu kutsen neman shugabanci da su maraywa Alhaji Muhammed Ibrahim 86 baya domin a cigaba da gudanar da aiyukan kungiyar yadda ya kamata domin samun hadin kai a tsakanin membobin kungiyar ba tare da ana samun rarrabuwar kaiba. Saboda haka in suna kishin yankin arewa da Najeriya da kuma kungiyar yan kasuwa na yankin arewacin Najeriya ya kama suyiwa Alhaji Muhammed Ibrahim 86 muba ya a domin ganin ya samu nasaran gudanar da aiyukan cigaban kungiyar ba tare da cikasba. Kawo yanzuma kungiyar na kokarin fadada aiyukanta na bude rassanta a dukkanin kananan hukumomi dake yankin arewacin Najeriya a wani mataki na inganta tare da cigaban yankin arewacin Najeriya baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.