An ja hankalin kwamishinoni wajen gudanar da aiyukan cigaban jahar Adamawa.
Mataimakiyar Gwamnan jahar Adamawa,
Farfesa Kaletapwa Farauta ta karanto sabbin komishinoni da aka nada dokar hana tarzoma.
Hakan na kunshene a a cikin wata sanarwa wanda sakataren watsa labarai mataimakiyar gwamna Hussaini Hammangabdo ya fitar a yola.
Farfesa ta shaidawa kwamishinonin cewa da suyi amfani da mukaminsu wajen cigaban jahar baki daya.
Da take jawabi a wurin wani taron da kayi da kwamishinonin a yola Farfesa Farauta tace gwamnati tana iya kokarinta domin gudanar da aiyukan cigaban jahar. Tare da kiransu da su gudanar da aiyukan su yadda ya kamata a wani mataki na cigaban jahar.
Ta kuma baiyana cewa kyakkawar gwamnati da aka zaba tana yin duk abinda zai kawo cigaba dama zaman lafiya.
Tace su sani gwamnati tana da manufofin da takeso ta cimma wadanda suka hada da inganta tsaro, bada ilimi kyauta, samarwa matasa aikinyi, saboda akwai bukatar baiwa gwamnati hadin kai da goyon baya domin ganin ta samu nasaran gudanar da aiyukan cigaba.
Don haka kyawawan manufofi takwas ne wannan gwamnati maici takeso taga ta aiwatar dasu . domin cigaban al ummar jahar.
Comments
Post a Comment