An kaddamar da fara aluran riga kafain kansar mahaifa wanda za ayiwa yaran mata da shekarunsu ya kama daga 9-14 a fadin jahar Adamawa.

A daidai lokacin da Najeriya ta fara gudanar da gagarumin aikin allurar riga-kafin cutar kansa mahaifa wato Human papillomavirus, HPV, a wani yunkuri na rage radadin cutar sankarar mahaifa, Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya bukaci iyaye da masu kula da su da su baiwa ‘ya’yansu da suka cancanta domin tabbatar da cewa sun samu alurar riga kafi. Gwamna fintiri ya bukaci hakane a lokacin da yake jawabi a bikin kaddamar da aluran rigakafin cutar ta HPV ga duk mata masu shekaru tara zuwa sha hudu a Yola jihar Adamawa. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri wanda mataimakiyar gwamnan jihar Adamawa, Farfesa Kaletapwa George Farauta ta wakilta ta yabawa kokarin hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar Adamawa da ma’aikatar lafiya ta jihar bisa rawar da suke takawa wajen gudanar da ayyukan tun kafin a fara aiwatar da ayyukan riga kafin, sannan ya bukaci iyaye da masu kulawa sun tabbatar da cewa 'ya'yansu da suka cancanta sun karbi rigakafin HPV. Da yake bayani kan labarun da ba tushe da allurar rigakafin cutar ta HPV, kwamishinan lafiya, a maikatar kiwon lafiya ta Jihar, Felix Tangwami, ya ce cutar sankarar mahaifa ita ce ta uku mafi yawan cutar kansa a tsakanin matan Najeriya, kuma itace ta biyu da ke haddasa mace-mace masu alaka da cutar daji a tsakanin ‘yan shekara 15 zuwa 44, don haka ya shawarci iyaye da su tabbatar da ‘ya’yansu suna yin allurar rigakafi. A jawabin bude taron, babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar Adamawa, Dokta Suleiman Sa’idu Bashir, ya bayyana shirye-shiryen kaiwa ga adadin ‘yan matan da aka yi niyya da rigakafin cutar ta HPV, domin rage yawan kamuwa da cutar kansar mahaifa a jihar. Yayin da suke yaba kokarin hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar Adamawa wajen tabbatar da kare lafiyar ‘yan kasar daga cututtuka da za a iya rigakafin su, Wakilan abokan huldar su, Asusun gaggawa na majakisar dinkin duniya UNICEF da sauran su sun bayyana cewa tabbatar da lafiyar ‘ya’ya mata na da matukar muhimmanci kuma ya roki tafiya tare da shugabannin addini da na gargajiya wajen gudanar da aikin rigakafin HPV. Abokan huldan sun bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta sa allurar rigakafin cutar ta HPV a cikin tsarin rigakafi na yau da kullun, da za a yi wa yara mata sama da miliyan bakwai allurar rigakafi a zagaye guda da ya kasance mafi girma a yankin Afirka a kokarin da ake sa ran zai rage yawan kamuwa da cutar kansar mahaifa da kuma ceto rayukan Matan Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE