An shawarci matasa da su bada tasu gudumawa wajen Samar da hadin Kai da zaman lafiya a tsakanin Al umma.
A wani mataki na samar da hadin kai da zaman lafiya a tsakanin matasa kwamandan rundunan tsaro ta operation SAFE HAVEN dake jahar Jos Major Gen. AE Abubakar ya shawarci matasa wadanda suka fito daga jihohin Filatau, Kaduna da jahar Bauchi da sukasance masu gudanar da aiyukan da zaikawo hadin kai dama zaman lafiya a tsakanin al umma.
Kwamandan ya bada shawaranne a lokacinda a kammal wasan kwallon kafa wanda rundunan ta shiryawa matasan a filin wasana Rwang Pam dake cikin garin Jos.
Kwamandan wanda shugaban ma aikatan rundunan ta SAFE HAVEN Brig. Gen. A A Egbejule ya wakilta yace an shirya da zumar samar da inganceccen zaman lafiya hadin kai dama cigaba a tsakanin rundunan da Al umma.
Don haka ya kirayi matasan da su tabbatar sun bada nasu gudumawar wajen samar da zaman lafiya da hadin kai da kuma cigaban jihihin.tare da shawartarsu da sukaucewa duk abinda zaikawo tashin hankali da rashin tuwa a tsakanin jama a.
Ya kuma kirayi daukacin al umma da sukasance suna taimakawa Jami an tsaro inganceccen bayanai da zaau taimaka wajen dakile aiyukan masu tada kayan baya.
Tunda farko a jawabinsa ko odinatan shirya wasan kwallon kafa Mr Victor Datur yace an shirya wasan ne domin ganin matasa sun samu kwarewa a harkokin wasanni a cikin jihohi dama kasa baki daya.
A yayin kammala wasan kwallon kafan dai kungiyar wasa na karamar hukumar Kanke a jahar Filatau ita tazo na daya bayan ta doke abokiyar karawanta na karamar hukumar Jema a dake jahar Kaduna.
Ita kuwa karamar hukumar Sanga ita tazo na uku bayan ta doke takwaranta ta Tarawa Balewa dake jahar Bauchi.
Bikin ya samu halartan manyan dama Jami an gwamnati da dai sauransu.
Comments
Post a Comment