Babban sifeton yan sandan Najeriya zai jagoranci tawagan yan sanda domin halartan babban taron kan tsaro a kasar Amurka.

Babban sifeton yan sandan Najeriya na riko Kayode Adeolu Egbetokun ya jagoranci manyan Jami an rundunan yan sandan domin halartan babban taro da akeyi a hihohin San Diego, da California na kasar Amurka. Wanda za a tattauna batutuwa da dama domin zakulo hanyoyin inganta tsaro a fadin duniya. Kakakin rundunan yan sandan na kasa ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja. Taron wanda tunin aka fara daga ranan 14 zuwa 17 ga watan oktoban nan da muke ciki, wanda kuma za a samu halartan manyan Jami an yan sanda daga sassa daban daban dake fadin duniya inda za tattauna yadda za a dakile aiyukan laifuka da ake aikatawa da suka hada da damfara ta yanan gizo, da dai sauransu. Batun samar da dabaru da inganta aiyukan tsaro domin bada kariya ga al umma duk suna cikin batutuwa da za a maida hankali akansu a wurin taron. Kuma a yau ne ake saran Babban sifetan yan sandan Najeriya Kayode Adeolu zai gana da Mr Todd Brown mataimakin sakateren harkokin tsaron Amurka domin samar da dabarun dakile aikata ba daidaiba a tsakanin jama a. Harwayau taron zai samu halarta kwararru daga fannini daban daban dake cikin Jami an tsaro domin kawo karshen kalu balen tsaro dake addabar Al umma.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.