Babu matsalar shugabanci a cikin kungiyar yan kasuwan yankin arewacin Najeriya .....Gambo Uban Nura.

An baiyana cewa kungiyar yan kasuwar arewacin Najeriya na nan daram kanta a hade yake ba wani matsalar tattare da kungiyar. Shugaban kungiyar na shiyar jahar Adamawa Alhaji Gambo Uban Nura ne ya baiyana haka a lokacinda yake magana dangane da kutse da wasu keson yiwa kungiyar a matakin kasa, wadanda kuma bazasu samu nasaraba da yardan Allah. Alhaji Gambo Uban Nura yace wasu ne kurum ke kokari kawo rudani a shugabancin kungiyar. Saboda haka ba abinda ya samu kungiyar komai yana tafiya dai dai karkashin jagorancin Alhaji Muhammed Ibrahim 86 kuma ba abinda zai taba shugabancinsa har sai ya kammala wa adinsa na shekaru hudu akan shugabancin kungiyar a matakin kasa. Gambo Uban Nura yace duk da cewa ba a rasa wasu matsaloli a kungiyar to Amman sukam Alhaji Muhammed Ibrahim 86 suka sani a matsayin shugaban kungiyar yan kasuwa na arewacin Najeriya saboda su suka zabeshi kuma dukkanin shuwagabanin kungiyar na jihohi sun amince da shi. Don haka ba wani shugaban kungiyar in ba Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ba. Ya kara da cewa bai kamata ace wasu suna baiyana Kansu a matsayin shuwagabanin kungiyarba su bari was adin wanda yake kai ya cika in sunaso sai su shiga zabe kamar yadda dokan kungiyar ya tanada. Da wannan ne yake kira ga dukkanin membobin kungiyar da suyi watsi da duk wani abinda zai kawo nakasu aci gaban kungiyar su kuma marawa Alhaji Muhammed Ibrahim 86 baya da bashi hadin kai domin cigaban kungiyar a fadin Najeriya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.