Gidauniyar Attarahum ta yabawa sanata Aisha Dahiru Binani.
Kungiayr Attarahum Foundation na mika godiyarta ga sanata Aishatu Dahiru Binani bisa kyautar mota kiran foma da ta baiwa kungiyar.
Kungiyar ta Attarahum Foundation tayi yabon ne a wata sanarwa da ta fitar dauke da sanya hanun shugaban kunguyar a jahar Adamawa Malam Mukhtar Dayyib a. yola, fadar gwamnatin jajar Adamawa.
Kungiyar a madadin shuwagabanin kungiyar dama membobin kungiyar na mika dinbin godiyarsu da farin cikinsu dangane da wannan taimako da sanata Aisha Binani tayi musu.
Sanarwa tace gidauniyar ta nuna goyon bayan ta tare da jinjinawa sanata Aisha Binani bisa na mijin kokari da takeyi na taimakwa kungiyoyi dama dai dai kun al umma baki daya.
Kunguyar ta kuma gudanar da adu o i na musamman domin nemana taimakon Allah da ya bada nasara a dukkanin abinda tasa agaba.
Comments
Post a Comment