Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jahar Adamawa ya kirayi kwamishinoni da manyan sakatarori da su bada tasu gudumawa domin cigaban jahar ta Adamawa

Gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya ja hankalin komishinoni da sakatarorin dindindin na jahar da su sa kula kan kudade da suke kashewa a ofisoshin su da ma rawa da suke takawa a matsayin su na manyan jami’an gwamnatin shi. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yayi wannan kira ne yayin da yake jawabin bude taron karawa juna sani na komishinoni da sakatarorin din din din na jahar mai taken: DAURAWA KAN SHUGABANCI MAI KYAU: MATSALOLI DA KUMA HANGEN GABA WA JAHAR ADAMAWA wanda ya wakana a birnin yola fadar jahar Adamawa. Gwamnan Ahmadu Umaru Fintiri yace ba zai yi haba haba ba gurin kin amincewa da bukatun kudade da za su jefa jahar cikin bashi , tare da jaddada cewa a kokarin gwamnatin shi na kawar da duk wani tarko da zai abka su cikin rashawa, da kuma bullo da wani tsari na fahimtar matakan da zaiiya domin cigaban.jahar Adamawa. Gwamna Fintiri yace a duk lokacin da ya Samu daman ganawa da jami’an gwamnati, yana kokari gurin tunatar da su cewa duk da sun bullo daga bangarori daban daban, mubayi’ar su ya kasance a kan al’umma da suka dau rantsuwar hidimta wa kuma kar su manta da cewa sun dau rantsuwa gwamnati data dau alkawarin tabbatar da adalci, jajircewa, hadin kai, zaman lafiya da ci gaban jahar. Yayin da ya tunatar da su alkawura da aka dauka a lokacin gangamin neman kuri’a, gwamnan ya kiraye su da su saje cikin wannan yunkurin kawo sauyin, inda yace duk wata ma’aikata ko hukuma ko cibiya dake karkashin ta na da damar sama wa gwamnati kudin shiga, ya kuma kiraye su da su tabbatar da cewa duk wani kudin gwamnati da ya samu ta hannun su, su saka shi a asusun bai daya na TSA. Gwamnan ya kuma kara jaddada anniyar gwamnatin shi na daurawa kan aiyuka da aka faro, aiyuka da aka faro su da kyawawan niyya da aka dau alwashin tafiya da kowa da kuma taba komai, tare da Karin cewa gwamnati ta sabunta manufofin ta zuwa takwas a suka hada da kare rayuka da kadarori, Ilimi da gina al’umma, kiwon lafiya, sabunta birane da gine gine, sifiri, noma, matakan tabbatar da abinci, samar da ruwan sha a birane da karkara, da kuma muhalli da sauyin yanayi. Ya kuma shawarci komishinonin da sakatarorin dindindin da su dau wannan taro da muhimmanci ganin gwamnati na jiran sakamakon taron domin ci gaban jahar Adamawa. Tun da farko dai a jawabinsa na maraba, sakataren gwamnatin jaha, Auwal Tukur yace makasudin wannan taron shine baiwa jami’an gwamnati damar bada tasu gudummowa domin tabbatar da jahar Adamawa da al’umma ke sha’awa. Da yayi jawabin godiya a madadin wadanda suka shirya taron, shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Dakta Edgar Amos ya godewa gwamnatin jaha da wadanda suka taimaka mata gurin shirya wannan taro, wanda ya zo a kan lokaci kuma hakan zai tamaka gurin ci gaban jahar. Taron komishinoni da sakatarorin din din din na kwanaki ukun gwamnatin jahar Adamawa ce ta shirya tare da tallafin kungiyoyin kasashen waje na USAID da GIZ.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE