Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya yaba da hukuncin da kotun sauraren koke koken zabe ta yanke.
Gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya bada yakinin cewa sashin shariya a Najeriya itace dama da kaahe ga jama a.
Gwamna Ahmadu Fintiri ya baiyana hakane a lokacinda yake mayar da martani dangane da hukuncin da kotun sauraren koke koken zabe ta yanke wanda ta baiwa gwamna Fintiri da cewa shine yayi nasara a zaben gwamna da aka gudanar .
Acewar gwamna Fintiri yace abinda da ya shaida a yau shine gaskiya tayi halinta kuma ya nuna cewa sashin shariya na gudanar da aiyukanta yadda ya kamata domin cigaban kasa dama al umman Najeriya.
Gwamna Fintiri yace wannan shariya ya kawo karshen duk wasu shakku dangane da zaben gwamna da aka gudanar saboda haka za a cigaba da gudanar da aiyukan cigaban al ummar jahar ta Adamawa baki daya.
Gwamnan ya kuma godewa Alkalain da suka jagoranci zaman kotun sauraren koke koken zaben karkaahin jagorancin mai ahariya Theodora Obi Oloho bisa jajircewa da sukayi wajen yanke hukunci.
Ya kuma tabbatarwa al ummar jahar Adamawa cewa gwamnatisa zata tafi da kowa domin gudanar da aiyukan cigaban jahar.
Comments
Post a Comment