An bukaci masu rike da mukamai masu bada sharawa gwamna da su riki mukamin da daraja.
Gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya ja hankalin masu mukamin masu bada shawara na musamman da su dauki nadin nasu da muhimmanci domin ci gaban jahar.
Gwamnan Ahmadu umaru Fintiri ya baiyana haka ne yayin rantsar da Salisu Zumo a matsayin mai bashi shawara na musamman, a wata biki da ta wakana a ofishin gwamnan dake gidan gwamnati dake yola fadar gwamnati jahar.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yace gwamnatin shi ta mayar da hankali ne gurin ci gaban yan jahar adamawa ganin a halin yanzu sun fi bukatar haka a kan komai.
Gwamnan yace ci gaban al’umma na kan gaba a gwamnatin shi, hakan ya sa ake bukatar masu basira irin su Salihu Zumo su shigo domin taimaka wa gwamnati domin tayi nasara.
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yace gwamnatin shi ta kudiri anniyar ganin ta daukaka al’ummar jaha zuwa mataki na gaba, tare da Karin cewa gwamnatin tayi nasarori da dama tun daga shigowar ta shekaru biyar da suka gabata.
A cewar gwamnna, wannan kokari na gwamnatin na bada sakamako da ake bukata ganin yanzu jahar ne na biyu a jerin sunayen jahohi da suka yi zarra a zana jarrabawan kammala sakandare wato WAEC da necco zuwa mataki na biyu, sabanin matakin da gwamnati mai ci ta samsu daga ta shekaru biyar da suka shige, a matsyi na 33, wani ci gaba da yayi ikirarin zai isa dukkan fannonin jahar domin ci gaban ta.
Gwamna Ahmadu Fintiri wanda ya baiyana Salihu Zumo a matsayin wanda mutanen shi dama al’ummar jahar Adamawa ke so, ya bukace shi da ya zo da kwarewarshi domin kari kan nasarori da gwamnati ta cinma domin cinma nasarar samun Adamawa da ake yakini.
Yayin da yake taya shi murnan wannan nadi, gwamnan yayi amfani da wannan dama gurin kiran shi da ya guji duk wani yanayi dake da nasaba da rashawa, ganin wannan gwamnati ta shimfida daukan matakai da za su hana rashawa musamanma
yayin da take ci gaba aiyukan gina jahar dama ci gaban al’ummar ta.
Da yake jawabi, mai bada shawara na musamman , Salihu Zumo ya gode wa gwamnan da wannan dama da ya bashi domin ya hidimta wa al’ummar jahar Adamawa, ya kuma dau alwashin zai yi iya kokarin shi domin ci gaban jahar Adamawa.
Babban Antoni janar na jaha kuma komishinan shari’a, Barista Afraimu jingi ne ya ratsar dashi, a wata yar karamar biki da ya wakana a ofishin gwamnan, inda sakataren gwamnatin jaha, Auwal Tukuku, da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Edgar Emos da dai saura su suka samu damar halarta
Comments
Post a Comment