Gwamnatin jahar Adamawa ta bukaci da al ummar jahar su maida hankalin wajen yiwa jaha dama kasa adu o i.

Gwamnan jahar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya kirayi daukacin al ummar jahar Adamawa, tare da yan uwa da abokan arziki da su kaucewa taruwa da niyar yin bikin ranan haifuwarsa a ranan Jumma a 27-10-2023. Gwamnan Ahmadu Fintiri yace mai makon haka ya kamata ayiwa jahar Adamawa da kasa baki daya adu o I, ya kara da cewa Al umma suna bukatan tainakon gaggawa biyo bayan matsalar tattalin arziki da ake fama da shi sakamokon cire tallafin mai fetur da akayi. Babban sakataren watsa labarai gwamnan Humwashi Wonosiko ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yola. Sanarwa tace mai girma gwamnan yace wannan yanayi da ake ciki na tsadar rayuwa wanda jama a ke fuskata wanda kuma hakan ya shafi tattalin arziki dama tsare tsaren gwamnatin tarayya. Domin magance matsalar a kwai bukatan a hada kai da kuma yin aiki tare domin samar da zaman lafiya da cigaban jaha dama kasa baki daya. A cewar gwamna Fintiri ba maganan bikin ranan haifuwa ne a gabanshiba, Al ummar jahar Adamawa ne a gabanshi saboda haka zaiyi dukkanin abunda suka dace domin ganin Al ummar jahar sun zauna cikin walwala. Harwayau gwamnan ya bada umurni yin adu o i a masallatai a ranan Jumma a da kuma a mujami u a rana lahadi domin neman taimakon Allah madaukakin sarki wajen kawo karshen kalubalen da aka fuskata sakamokon cire tallafin maifetur.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE