Gwamnatin jahar Adamawa ta shawarci hukumomin tsaro da sukasance masu aiki kafada da kafada domin dakile matsalar tsaro a fadin Najeriya.

Gwamnan jahar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya bada shawarar yawanta zama tsakanin cibiyoyin tsaro a matsayin daya daga cikin matakan dakile matsalolin tsaro dake addabar kasar nan. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya bada wannan shawara ne yayin da yake bude taron daraktocin cibiyar tsaro na farin kaya, DSS karo na goma sha uku da ya wakana a shalkwatar cibiyar tsaron na jahar Adamawa dake yola, fadar jahar. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya bada shawarin cewa kamata yayi cibiyoyin tsaro sun rika yawaita zama domin musanyar bayanai, tsara yadda za suyi aiki da ma shawo kan kalubale ko gibi da ake da su domin samar da zaman lafiya da tsaro. Gwamnan yace musanyan bayanai, atisayin hadaka da karawa juna sani tsakanin cibiyar tsaron farar kayan da takwarorin ta zai taimaka matuka gurin samar da cikakken bayanen yanayin tsaro da ake fama da shi a rewa maso gabas, kana atisayin zai karfafa kuzarin yadda za a rika tinkarar barazanonin tsaro kamar yadda ya kamata. Gwamnan wanda yace yankin arewa masu gabas na fama da matsalolin tsaro daban daban na tsawon lokaci da suke yiwa zaman lafiya da daidaituwa da ci gaba barazana a jahohi dake yankin dama kasa baki daya, ya kara da cewa yankin na ta baiwa hamata iska da kalubalen tsaro da suka daidaita al’ummomi, tare da barin al’umma cikin tsoro da dimuwa. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yace a jahar Adamawa musamman, an ja daga da bata gari , da ake kira yan shila, masu kwace wayoyin mutane dama jikkata su. Ya kuma kara jadddada matsayin gwamnonin yankin arewa maso gabas na baiwa cibiyar tsaron farin kayan hadin da ma sauran cibiyoyin tsaro a dukkan matakai domin samar da tsaro da da doka da oda a cikin al’umma. A jawabin shin na maraba, daraktan cibiyar tsaron farin kaya na jahar Adamawa, Hassan Adeleke yace yayin zaman na su zasu tattauna kan matsalolin tsaro da suka addabi yankin arewa maso gabas. Adeleke yace a karshen zaman nasu za su fitar da matsaya da suka cinma da kuma matakai da aka dauka domin gudanar da aiyukan su a yankin dama sauran masu ruwa da tsaki. A sakonnin sun a godiya, komandan dakarun soji na 23 armored Briget dake yola, Brigediya janar Mohammed Jibrin Gambo da komishinan yan sanda, Babatola Afolabi sun tabbatar da bada tasu goyon baya domin aiki tare da sauran cibiyoyin tsaro gurin ganin an samu zaman lafiya a fadin kasa. Cikin abubuwa da suka wakana yayin bude taron sun hada da baiwa gwamna Fintiri kambun yabo, na irin goyon baya da yake baiwa cibiyar tsaron farin kaya na DSS .

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE