Gwamnatin jahar Gombe ta taya Alhaji Jalal Arabi murnan samun mukamin shugaban hukumar aikin Hajji ta kasa wato NAHCON.

Gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya ya yaba da yadda aka nada dan jahar ta Gombe Alhaji Jalal Arabi wanda shugaban kasa ya Bola Tinubu ya nada a matsayin shugaban hukumar aikin Hajji ta kass wato NAHCON. Gwamana Muhammadu Yahaya ya yaba tare da godewa shugaban kasa Bola Tinubu bisa nada dan Asalin jahar Gombe Alhaji Jalal Arabi inda ya baiyana nashi a matsayin wanda ya cancanta kuma mutunne wanda yasan makaman aiki. Gwamnan ya baiyana hakane a wata sanarwa wanda darectan watsa labarain gwamnan Ismaila Uba ya fitar a jahar Gombe. Sanarwa tace Alhaji Jalal yana da kyakkyawa tarihi wanda yayi ritaya a matsayin babban sakatare tararayya. Gwamnan ya shawarceshi da ya gudanar da aiyukansa bil hakki da gaskiya domin samun cigaban hukumar yadda ya kamata. Sanarwan ta kara da cewa nada Alhaji Jalal Arabi abun alfahari ne ga jahar Gombe kuma jahar zataji kunyaba domin kuwa Alhaji Arabi mutumne da ya kware da kuma hazaka wajen gudanar da aiyukan cigaba. Saboda haka a madadin gwamnati dama daukacin al ummar jahar ta Gombe gwamnan ya taya shi murna samun wannan matsayi kasancewarsa dan asalun jahar ta Gombe.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.