Gwamnatin jahar Kano ya kudiri aniyar tura dalube Sama da dubu Daya kasashen waje domin karo karatu.
jahar Kano Abba Kabir Yusuf yace gwamnatinsa zata dauki nauyin karatun dalube akalla 1,001wadanda zasuyi karantun digiri na biyu a Jami o I daban daban dake fadin duniya.
Gwamnan ya baiyana hakane a lokacin kaddamar da shirin Kai dalube karatu kasashen waje karatu Wanda ya gudanar a gidan gwamnati dake Kano.
Gwamnan yace tawo da Shirin Samar da gurbin karo karatu a kasashen waje yana daga cikin cika alkawarin da yayi a lokacinda yake Neman zabe.wanda Kuma yace lamarine da ya rataya akan gwamnati.
Ya Kuma baiyana cewa wadanda suke dauke da digiri na farkone zasu ci gajiyar Shirin da zasuyi karatu a kasashen Indiya, da dai sauransu.
Wadanda suka anfana da Shirin sun nuna godiyarsu da Jin dadinsa dangane da damar da aka basu domin samun gurbin karo karatu a kasashen waje.
Comments
Post a Comment