Hukumar masuyiwa kasa hidima ta NYSC shawarci direbobi dangane da tafiye tafiyen dare.

A kokarinta na magance matsalar tafiyar dare hukumar masuyiwa kasa hidima wata NYSC ta daukin aniyar wayarwa direbobi kai dangane da tafiye tafiyen dare. Ko odinatan hukumar a jahar Taraba Anthony Nzoka ne ya baiyana haka a lokacinda ya jagoranci tawagan masuyiwa kasa hidma zuwa tashan motoci domin wayarwa direbobi kai da su kaucewa tafiya dare. Tawagan sun ziyarci Babbar tashar jaharTaraba domin fadakar da fasinja dama direbobi dangane da matsalar da tafiyar ke tartare da shi. E
Tawagan dai sun rarraba Kansu domin ganin sun isar da sakon yadda ya kamata a fadin jahar inda suka bukaci direbobin dama fasinja da sukasance masu kare rayukansu ta kaucewa tafiyar dare inda aka shawarci matafiya da su hakura da zaran Shida na gamma in yayi. Ko odinaton ya kirayi direbobi da su tsaya da zaran suna jin barci musammanma in sukazo wucewa a kusa da ofishin yan sanda, barikin soja, ko kuma kusa da duk sakatariyar hukumar ta NYSC. Mr Anthony Nzoka ya kirayi membobin masuyiwa kasa hidima da suma sukasance masu maida hankali wajen kula da lafiyar hanyoyi a koda yaushe. Ya kuma yi adu a Allah ya kare tare da tabbatar da cewa hukumar ta NYSC a shirye take ta hada kai da tashoshin motoci dake fadin jahar.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE