Kungiyar ma aikatan majalisar dokokin jaha PASAN ta bi sahun uwar kungiyar wajen shiga yajin aiki.

Kungiyar ma aikatan majalisar dokokin jihohi shiyar jahar Adamawa PASAN tabi sahun uwar kungiyar ta kasa wajen shiga yajin aikin Illa masha Allah na kasa baki daya, biyo bayan rashin aiwatar da kidirin dokan cingashinkansu dangane da kudi majalisar dokokin jihohi wanda yake cikin kundin dokan tarayya Najeriya. Shugaban kunguya ta PASAN a jahar Adamawa Idris Sali ne ya baiayana haka a lokcin ya jagiran taron da kungiyar ta gudanar a harabar majalisar dokokin jahar Adamawa, yace rashin aiwatan da dokan da gwamnati tayi wanda hakan yasa suka dauki tsawon lokaci suna dako. Shugaban yace duk dacewa anacigaba da tattaunawa a tsakanin kungiyar da gwamnati a matakim kasa wanda suke sa tsammanin cewa za a samu sakamokon da zata haifar da da mai ido domin kungiyar gwamnoni sun fara duba lamarin. Ya kuma koka da yadda wasu jihohin suna fuskantar irin wadannan kalubale na rashin aiwatar da basu yancin gaahin kansu a matsayinsu na ma aikatan majalisar dokokin jahar a inda jahar Adamawa ma ba a barta a bayaba. Yanzu haka dai suna jiran sakamokon tattaunawa da kungiyar keyi da gwamnati a mataki kasa don haka Idris Sali ya umurci membobin kungiyar da su kauracewa wuraren aikinsu har sai an biya musu bukatunsu.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE