Kungiyar yan Jarida a Najeriya shiyar jahar Adamawa ta taya Gwamna da mataimakiyatsa murna samun nasara a kotun sauraren koke koken zaben gwamna.

Biyo bayan da kotun sauraren koke koken zaben gwamna Wanda tayi zamanta a yola Kuma ta yanke hukunci baiwa gwamna maici wato Ahmadu Umaru Fintiri nasara. Alkalai uku karkashin jagorancin maishariya Theodora O Uloho inda suka yanke hukunci cewa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ne halacceccen zaben gwamna jahar Adamawa. Hakan yasa kungiyar yan Jarida a Najeriya N U J shiyar jahar Adamawa tana taya Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri murnan nasara da ya samu a kotun sauraren koke koken zaben gwamna wacewar kungiyar dai wannan hukunci nasarace ga Al ummara jahar Adamawa. Nasaran gwamna Fintiri ya nuna cewa sashin shariya na nan daram wajen gudanar da adalci wa Al umma da kuma bin doka da oda a jahar dama kasa baki daya. Kungiyar ta baiyana haka ne a sakonta na taya murna ga gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da fitar dauke da sanya hanun sakateren kungiyar ta N U J a jahar Adamawa Fedelis Jockthan. Da wannan ne kungiyar take taya Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri tare da mataimakiyatsa Farfesa Kaletapwa George Farauta murnan samun nasara domin tabbatar musu da kujeransu. Tare da kiran yan adawa da suzo a hada kai domin gudanar da aiyukan cigaban dama Al umma jahar ta Adamawa baki daya. Harwayau kungiyar yan Jarida a jahar Adamawa ta kirayi daukacin Al ummar jahar ta Adamawa da sukasance masu bin doka da oda a Koda yaushe da Kuma gudanarwa gwamna dama gwamnati adu o i Samar da zaman lafiya dama cigaban jahar baki daya. A cewar sanarwan dai gwamna Ahamadu Umaru Fintiri ya jajirce wajen wanzar da zaman lafiya da Kuma gudanar da kyakkawar gwamnati da Kuma nuna shugabanci na gari Wanda Kuma hakan ya kawo cigaba yadda ya kamata. Maigirma gwamna ka karbi gausuwar shugaban kungiyar yan Jarida na jahar Adamawa Kwamuret Ishaka Donald Dedan dama Majaliaar membobin kungiyar baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE