Kungiyar yan kasuwan Yankin Arewacin Najeriya tace itakam ba wani rikicin shugabancin a cikin kungiyar.
An bukaci ya yan kungiyar yan kasuwar arewacin Najeriya wato Arewa Traders Association of Nigeria ATAN da su kasance masu hada kansu a koda yaushe domin samun cigaban kunguyar a Najeriya baki daya.
Shugaban kungiyar a shiyar jahar Bauchi kuma sakataren tsare tsaren kunguyar na yankin arewa masau gabashin Najeriya Alhaji Abdullahi Y Muhammad wanda akafi sani da (Abdallah Caps). ne ya baiyana haka a lokacinda yake jawabi dangane da kutsen shugabanci da wasu keyiwa kungiyar a matakin kasa.
Alhaji Abdullahi Y Muhammad yace ba dai dai bane ace ana samu rashin dai dai to a tsakanin shuwagabani kungiyar wanda hakan zaikawo koma bayan aiyiukan kungiyar.don haka ya kamata shuwagabanin kungiyar sukasance tsintsiya madaurinki daya domin kai kungiyar tudun na tsira.
Alhaji Abdullahi kira yayiwa shuwagabanin da sukasance masu hada kasu da kuma yin dukkanin abinda suka dace domin kawowa yan kasuwa cigaba domin bunkasa harkokin kasuwanci a yankin arewacin Najeriya.
Saboda haka ya dace mu baiwa shugabancin Alhaji Muhammed Ibrahim 86 hadin kai da goyon baya kasancewa shine zababben shugaba wanda ya samu goyon bayan dukkanin shuwagabanin kungiyar na jihohri sha Tara dake yankin arewacin Najeriya. Kuma shine yake da takardan shaidan cin zaben shugabacin kungiyar.
Don haka mu bar duk wata rigima mai makon hakama ya kamata mu maida hankali wajen duk abinda zai kawo hadin kai da goyon bayon baya, mukuma yi hakuri domin ganin mukai ga samun nasaran duk abinda mukasa gaba.
Alhaji Abdullahi yace kungiyar tana da dokokinta kuma a dokan kunguyar idan aka zabi shuwagabani zasuyi wa adin shekaru hudune kuma shuwagabanin da suke kai a yanzu karkashi jagoranci Alhaji Muhammed Ibrahim 86 wa adinsu bai kareba saboda haka ba wani dalilin da yasa wasu zasu fita suce sune shuwagabanin. Wannan ba dai dai dashi
Saboda haka nema yake shawartan membobin kunguyar na yan kasuwar Arewacin Najeriya da suyi hakuri su marawa Alhaji Muhammed Ibrahim 86 baya da kuma yi masa fatan Alheri domin ganin ya samu nasaran cugaba da gudanar da aiyukan cigaban kungiyar. Mu dai a jahar Bauchi a matakin shugabancin arewa taraders association ba wanda muka sani a matsayin shugaban kungiyar ta kasa sai Alhaji Muhammed Ibrahim 86. Domin shine muke da hujja da shaidar cewa zababbene wanda dokan kungiyar dana Najeriya duk sun amince dashi.
Hakama dukkanin shuwagabanin kungiyar na jihohin arewacin Najeriya sha tara sun amince da shugabancin Alhaji Muhammed Ibrahim 86 kuma ba wanda aka sani sa shi Alhaji Muhammed Ibrahim 86.
Comments
Post a Comment