Kungiyoyi masu zaman kansu sun nemi da a bunkasa harkokin noma .

Wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun nemi da gwamnatin jahar Adamawa da ta kasance tana sanya ido kan aiyukan harkokin noma dama gudanar da shirye ahiryen abinda ya shafi harkokin noma domin inganta harkar noma a fadin jahar. Shirin wanda zai gudana kakashin hukumar inganta harkokin noma a Najeriya, IAA a cikin shekaru biyar da rabi wanda zai lashe dalan Amirka milyon 15.8 tare da hadin gwiwar cibiyar bunkasa harkan noma ta kasa da kasa IITA tare da cibiyar binciken dangane harkokin tsiro na kasa da kasa ICRISAT. Shirin zai taimakawa marassa galihu musammanma wadanda rikicin boko haram ya shafa saboda haka akwai bukatar a kara musu kwarin gwiwa cigaba da bunkasa harkokin noma yana daga cikin aniyar hukumar USAID domin ganin an farfado da tattalin arzikin arewa masau gabashin Najeriya biyo bayan tasku da ya shiga sakamokon hare haren masu tada kayan baya. Mataimakin shugaban kungiyar ta IAA Mr Olukayode Faleti shinema ya wakilci shugaban kungiyar Mr Prakash Silwa a wurin biki da ya gudana akan dubawa tare da farfado da darajan noma. Yace ya zuwa yanzu ana fuskantar girbe amfanin gona domin samun sakamokon abinda muka noma, saboda haka munkasance anan ne domin domin farkar da manoma yadda za su kula da gonakainsu. Ya kara da cewa aiyukansu yana daga cikin samar tsarin da zaitaimaka wa manoma a jihohin Adamawa, Borno, da kuma jahar Gombe. A cewarsa du da du manoma 175 ne suka amfana da shirin. a yayinda manoma 94 dag jahar Adamawa sai 75 daga jahar Borno, sai kuma shida daga jahar Gombe. Mr Faleti yace manoma sun samu karin ilimin sabbin dabaru da kuma aiki a aikace harma da fasaha domin ganin sun samu damar bunkasa harkokin noma. Gwamnatin jahar Adamawa ta sanar da cewa zatayi dukkanin mai yiwa domin tallafawa manoma musammanma a lokacin noman rani. Kwamishinan albarkatun noma na jahar Adamawa Farfesa David Jatau wanda ya wakilci gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ne ya Sanar da haka a lokacinda yake jawabi a wurin bikin taron da ya gudana a karamar hukumar Damsa dake jahar Adamawa. Hakimin Demsa Chief Fidelis Ali ya tabbatar da cewa manoman yankinsa dama masu wasa dayin noma saboda haka sun samu karin basira, da fasaha da zai taimaka musu wajen gudanar da harkokinsu na noma.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.