Rundunan yan sanda a jahar Adamawa tasha alwashin zakula masu aikata laifuka daga maboyarsu dake fadin jahar.
A kokarinta na dakile aiyukan ta addanci a fadin jahar Adamawa rundunan yan sandan jahar tayi nasaran kama wani mutum mai shekaru talatin da haifuwa mai suna Shuaibu Abubakar kuma an samu nasaran cafkeshi a wani samamen hadin gwiwar yan sandan da mafarauta suka kai a mabuyar yan ta addan.
Maihulda da jama a na rundunan yan sandan a jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yola.
Sanarwa tace akwai wani da ake zargi dake Tambo wanda kuma yana cikin jerin sunaye wadanda ake neman ruwa a jallo.
Rundunan ta kuma gano bindiga kiran Ak 47 da kuma arbarushe 16 a wurin wadanda ake zargi.
Kawo yanzu kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya baiyana farin cikinsa dangane da nasaran da rundunan tayi. Ya kara da cewa babu maboyar masu data kayan baya a jahar Adamawa domin kuwa rundunan ta dauki dukkanin abinda suka dace domin dakile aiyukan masu garkuwa da mutane a fadin jahar ta Adamawa baki daya.
Comments
Post a Comment