Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta lashi takwabin dakile aikata ta addanci a fadin jahar ta Adamawa.

A kokarinta na dakile aiyukan ta addanci a fadin jahar Adamawa rundunan yan sandan jahar yanzu haka tana tsare da wata mota mai dauke da rijistan Numba GME 235 AE wanda kuma an gano wasu kayaki guda uku a cikin motar. An samu nasaran kama motan ne a lokacinda Jami an yan sandan ofishin yan sanda dake Yolde Pate ke gudanar da sintiri akan titin da ta hada Yola da Yadim. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da yarabawa manema labarai a Yola, fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Sanarwan ta baiyana cewa a yayinda direbab motar ya hangi Jami an tsaro sai yayi kokarin kaucewa da ya samu matsin jami an tsaro sai ya tsallaka ya bar motar ya gudu. An gono wasu kayaki a cikin motar da suka hada da tsarka, makulli, wato kwado, da dai sauransu. Wanda kuma ana zargin yana amfani da sune wajen yin garkuwa da mutane. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya tabbatar da cewa zasu dauki dukkanin matakai da suka dace domin ganin masu aikata laifuka baau samu damar gudanar da aiyukansuba a fadin jahar. Ya kuma kirayi daukacin al umma jahar Adamawa da sukasance suna baiwa rundunan bayanai tsirri akan lokaci domin ganin an samu damar damke masu aikata ta addanci a tsakanin al umma.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE