Rundunan yan sandan jahar Adamawa tasha alwashin inganta tsaro a fadin jahar Adamawa.

A wani mataki na samar da dabaru dama inganta tsaro rundunan yan sandan jahar Adamawa ta bauyana aniyarta na hada kai da masarautun gargajiya, yan banga mafarauta da dai sauranasu domin dakile aiyuka ta addanci a tsakanin Al umma. Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya tabbatar da cewa rundunan a shirye take ta takawa dukkanin aiyukan ta addanci birki dama sauran kalubalen tsaro a fadin jahar ta Adamawa baki daya.
Kwamishinan ya baiyana hakane a ranan talata 24-10-2023 a lokacinda yake jawabi a ofishin rundunan dake Karewa a cikin karamar hukumar yola ta arewa a ganawa da yayi da masu ruwa da tsaki da manyan Jami an yan sandan harma da yan banga domin yaki da masu aikata laifuka a fadin jahar. Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Sanarwa tace kwamishinan yace rundunan yan sandan zata jagoranci ganin cewa dukkanin ofishoshin yan sandan domin tabbatar da cewa sun dakile aikata laifuka a yan kunansu kuma rundunan sata saka kafar wando daya da duk maiyiwa doka karan tsaye. Kwamishinan ya yabawa Hakimin Karewa dana Jimeta bisa goyon baya da suke baiwa rundunan yan sanda dama yan banga wanda hakan zai taimaka wajen kare rayuka dama dukiyoyin Al umma na ciki da wajen fadar jahar. Kwamishinan ya kuma kirayi Jami an yan sandan da sukasance masu amfani da bayanai da suke samu wanda shima yana daga cikin dakile aikata barna. Harwayau kwamishinan ya kirayi daukacin Al ummar jahar Adamawa da akoda yaushe sukasance suna taimakawa rundunan yan sandan domin samun nasarn cafke masu aikata laifuka a tsakanin Jama a. Ya kara da cewa rundunan a shurye take tacigaba da hada kai da sarakunan gargajiya, takwarorinta na hukumomin tsaro , mafarauta,yan banga domin inganta tsaro a fadin jahar ta Adamawa baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.