Rundunan yan sandan jahar Gombe tayi nasaran kama wadanda ake zargi da aikata laifuka daban daban a fadin jahar.

Rundunan yan sandan jahar Gombe ta laahi takwabin inganta tsaro domin kare rayuka da kuma dukiyoyin Al umma a fadin jahar Gombe, acewar rundunan dai zatayi aiki kafada da kafada da shuwagabanin al umma dama masu ruwa da tsaki domin ganin anbi doka da oda a fadin jahar baki daya. A yanzu haka ma rundunan tana tsare da wani matashi da ake zargi da kaahe wata mai suna Hajiya Aisha Abdullahi Aka Damori, da wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane da kuma kisan kai, sai kuma mutane uku da ake zargi da dayin fashi da makami a yayinda biyu kuma ake zarginsu da aikata fyade. Kakakin rundunan yan sandan jahar Gombe Mahid Mu azu Abubakar ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a jahar Gombe. Sanarwan ta baiyana cewa rundunan tana tsare da mataahin mai suna Mustafa Adamu Isa wanda akafi sani da (Abbati). Dan shekara 18 da haifuwa wanda ke zaune a anguwar jeka da fari a Gombe bisa zarginsa da kisan kai. A ranan 20-10-2023 ne da misalin karfe goma na dare ne dai wamin magidanci mai suna Muhammed Sani Abdullahi mai shekaru 45 dake jeka da fai ya kai rahoton zuwa ofishin yan sanda dake yankin Pantami cewa wani da ba asan ko wayeba ya yanka mahaifiyarsa da wuka. Wanda hakan yasa runduna yan sandan batayi da wasaba ta garzaya inda lamarin ya faru kuma da isa wurin sai ka taradda Hajiya Aisha kwance cikin jini nan da nan aka garzaya da ita zuwa Asibitin koyarwa ta tarayya dake jahar Gombe domin ceto rayuwarta amma daga bisani kitoci sun tabbatar da cewa ta mutu. Biyo bayan bincike da rundunan ta gudanar ne dai ya sa aranan 22-10-2023.ta kama wanda ake zargi da hallaka Hajiya Aishatu Abdullahi. A cigaba da bincike wanda ake zargin ya amsa lafinsa harma ya ambaton wani mai suana Idris Abubakar dan shekara 17 da haifuwa da taimaka masa wajen gudanar da wannan aika aika sai dai Shi Idris dan ya musanta cewa basan ko wayene ya kashe Aishatu ba. Wanda ake zarginda ya baiyana cewa Hajiya Aisha ta dawao cikin gida daga makwabtane dai ta sameahi a dankinta, ta tambayeshi ko me yakeyi a dakin nata yagaza wajen bata amsa daganan ne sai ya aukwa mata da wuka inda ya tsere ya barta cikin jini an kuma gano sifana a wurin wanda ake zargi. Shaidun gani da ido sun baiyana cewa a lokacinda lamarin ya faru Hajiya Aisha tayi ta ihu na neman taimako kuma kuma shi Idris din yayi ta kokari wajen kiran yan uwata ta waya lamarin ya cutura. Sai wanda ake zargin yace shi daya ya aikata laifi ya ambacin Idris dinne saboda shi yayi sanadiyar da aka koreshi a garejin wanda suna aiki tare. Rundunan ta kuma tsare da wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane domin nenan kudin fansa wato Rabilu Adamu dan shekaru 22 dake Gombe Abba a cikin karamar hukumar Dukku a jahar ta Gombe da Ado Yusuf mai shekaru 28 wanda ke kyauyen Zoro dake cikin karamar hukumar Darazo a jahar Bauchi. A ranan 20-10-23 wani suna malam Sadi Musa ya kai rahoto a ofishin yan sanda dake Karamar hukumar Dukku cewa wasu da ba asan ko suwayeba suka ahiga gidansa sukayi awun gaba da yaransa da shekaru uku daga bisani ya baiyana cewa yana zargin wani dan uwansa mai suna Rabi u Adamu biyo bayan rashin gamsuwa da lamarinsa bayan batan yaron. Daga jin wannan rahoto ne dai sai DPO yankin na Dukku ya jagoranci tawagan Jami an tsaro inda suka kutsa daji daokin farauto wadanda ake zargi, wanda kuma yahakn yasa akayi nasaran kama mutanen. Kuma a bincike da aka gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin bayan ya dauki dan uwan nasa ya hallakashi inda ya saahi a buhu kuma ya amsa laifinsa. Su kuma mutane uku ana zarginsune da yin faahi da makami wato sun hada da Kabiru Ibrahim wanda akafi sani da KB mai shekaru 25 da Usman Yahaya wanda akafi sani da Imamu dan shekaru 20 da kuma Adamu Auwal wanda akafi sani da Ahda . Bincike ya nuna cewa an kama mutanen ne a yayinda wasu ke wawuran kayaking jama a wanda hakan yasa aka kai rahoton aukuwar lamarin a ofishin yan sanda mai numba 999 inda nan take aka dauki matakin kai samamai wanda kuma akayi nasaran kamasu. Wadanda ake zargunsu da wasu mutane. An kuma gani kayaki da dama a wurin wadanda ake zargi da suka hada da kwanfitar hanu, wayoyin hanu da dai sauransu. Dangane da aikata fyade kuwa rundunan yan sanda tana tsare da wani mai suna Donal Joseph dake zaune a karamar hukumar Kaltungo bisa zarginsa da yiwa wata yarinya fyade kuma an kamaahine biyo bayan da wani mai suna Danjuma Jauro yakai rahoton cewa shi wanda ake zargi ya kai yarinyar go dansa inda yayi anfani da wannan damar wajen yi mata fyade. Kuma wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma nan bada dadewaba zasu gurfanar daahi gaban kotu domin ya fuskaci shariya. Shima Muhammed Auwak dan shekaru 40 wanda ke zaune a Riyal Bagadaza a jahar Gombe bai tsiraba don an kamaahi da laifin sata hakan ya faru ne bayan da Aliyu Muhammed wanda manajane na gidan buga ruwan pure water da biredi ya kai rahoton cewa an sace mota fijo kiran 406 kuma anyi nasaran kama wanda ake zargin tare da makullen fijo dana Honda. Rundunan ta kuma godewa manema labarai bisa hadin kai da goyon baya da suke baiwa rundunan yan sandan jahar Gombe. Rundunan ta kuma kirayi daukacin al ummar jahar Gombe da sukasance suna taimakawa rundunan tayi aiki tare domin kare rayuka dama dukiyoyin Al ummar jahar Baki daya.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.