Rundunan yan sandan a jahar Ogun tana tsare da dalube biyu bisa zarginsi da cinnawa kayakin makarantansu wutan.

Rundunan yan sandan jahar Ogun yanzu haka tana tsare da dalube biyu da ake zargi da cinnawa kayakin makarantarsu wuta, wato makarantar Firamare dake Isheri Olofin a jahar ta Ogun. Daluben da ake zargin sun hada da Wahis Musa dan shekaru 6 da haifuwa da kuma Malik Illiasu shi kuma yana da shekaru 9 da haifuwa dukkaninsu mazauna Isheri Olofin ne. Kakakin rundunan yan sandan na jahar Ogun Omolola Odutola ne ya sanar da haka a wata sanarwa da yarabawa manema labarai a Abeokuta fadar gwamnatin jahar Ogun. Kama daluben ya biyo bayan rahoton da ofishin yan sandan yankin Ojodu- Abiodun ya samu cewa Wahis Musa da Malik Illiasu sun shiga wani aji da ba a kulleba inda suka rinka tattara takardun makarantar a wari guda nan take suka cinnawa takardun wuta. Wanda kuma kawo yanzu ba a kai ga sanin yawan barnan da wutan tayiba. Daga samun rahoton haka Jami an yan sandan yankin na Ojodu- Abiodun basuyi da wasaba inda suka gaggauta isa wurin da lamarin ya faru, wanda hakan ya basu nasaran kama wadanda ake zargi da aikata lamarin. Ya zuwa yanzu dai rundunan yan sandan ta fara gudanar da bincike domin tattaunawa da iyayen yaran da suka aikata wannan laifi, kuma rundunan zata baiyanawa al umma sakamokon bincike da suka gudanar.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE