Rundunan yan sandan Najeriya zata gudanar da taro domin inganta tsaro a fadin Najeriya.

A kokarinsa na tabbatar da inganta tsaro a fadin Najeriya, Babban sifeton yan sandan Najeriya Kayode Adeolu Egbetokun ya gudiri aniyar ganin an samar da wadaceccen tsaro domin aiwatar da tsarin gwamnatin tarayya na samar da tsaro da dai sauransu. Hakan yasa Babban sifeton ya shirya taro na musamnan da za a yi da manyan Jami an yasandan dake fadin Najeriya wanda ana saran za a fara taro daga ran 30-10-2023 zuwa ran 1-11-2023 a Owerri dake jahar Imo. Kakakin rundunan yan sandan ta kasa ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar wanda aka rabawa manema labarai a Abuja. Taron wanda zai hada kan manyan Jami an yan sandan da suka hada da mataimakan Babban sifeton yan sandan Najeriya, kwamishinonin yan sandan,dama sauran wasu hukumomin tsaro da suma ake saran zau halarci taron. Wanda kuma haka zai bada dama ga rundunan yan sandan ganawa da takwarorinta domin ganin an inganta tsaro na ciki da wajen Najeriya domin samar da cigaba dama zaman lafiya mai daurewa. Da wannan ne Babban sifeton ya kirayi Jami an yan sandan da sukasance masu gudanar da aiyukansu bisa doka a wani mataki na tabbatar da tsaro dama aiyukan samar da cigaban a fadin Najeriya dai dai sauransu.

Comments

Popular posts from this blog

Rundunan yan sandan jahar Adamawa ta taimakawa iyalain Jamin an yan sanda da suka gamu da ajalinsu a bakin aiki.

Police in Adamawa Arrestet 31 year for serial theft.

Jambutu got new Chairman of PCRC.