Sakataren harkokin wajen Amurka ya gana da firaministan kasar Isra ila.

Karo na biyu a litinin din nan ne sakataren harkokik wajen Amurka Antony Blinken ya gana da firaministan kasar Isra ila a garin Tel Aviv. Tun a makon da ta gabatane dai sakateren harkokin kasar wajen Amurka ya gana da firaministan kasar ta Isra ila Benjamin Netanyahu bayan da Hamas ta kaddamar da hare hare masu karfi akan kasar ta Isra ila. Antony Blinnken ya tabbatar da cewa kasar Amurka zata baiwa kasar ta Isra ila goyon baya domin kasar ta kare kanta daga duk wani hari da za a iya kawo mata. Sama da Isra ilawa 1,400 ne dai suka hallaka a kwanaki tara da suka gabata biyo bayan da kungiyar Hamas ta kutsa cikin kasar ta Isra ila ta Gaza tare da kai hare hare lamarin da yayi sanadiyar mutuwar sojoji da fararen hula.

Comments

Popular posts from this blog

𝐀𝐃𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐏𝐎𝐋𝐈𝐂𝐄 𝐂𝐎𝐍𝐅𝐈𝐑𝐌 𝐅𝐀𝐓𝐀𝐋 MOTOR 𝐀𝐂𝐂𝐈𝐃𝐄𝐍𝐓 𝐈𝐍𝐕𝐎𝐋𝐕𝐈𝐍𝐆 𝐌𝐈𝐋𝐈𝐓𝐀𝐑𝐘 𝐕𝐄𝐇𝐈𝐂𝐋𝐄 𝐀𝐍𝐃 𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐑𝐂𝐈𝐀𝐋 𝐁𝐔𝐒

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

NSCDC Adamawa State Command Deploys 2,521 Personnel for Easter Festivitie