Shelkwatan rundunan yan sandan jahar Adamawa tana tsare da wani da ake zargi da garkuwa da mutane.
Rundunan yan sandan jahar Adamawa a yanzu haka tana tsare da wani matashi dan shekaru 25 da haifuwa mai suna Gaiya Mallam Usman bisa zarginsa da aikata yin garkuwa da mutane.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Ngyroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola fadar gwamnatin jahar.
Wanda ake zargin wanda ya fito daga Tambo a cikin karamar hukumar Girei a jahar Adamawa wanda ake zarginsa da wasu mutane hudu da yin garkuwa da mutane uku harma sun karbi kudin fansa nera milyon 8.
Sai dai wanda ake zargin ya baiyana cewa shikam dubu 470.000 kawai ya karba cikin milyon 8 daga iyalen wadanda aka yi garkuwa da su kuma ya baiyana cewa yayi amfani da kudaden ne wajen sayan kayakin sawa.
Kawo yanzu dai kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya baiwa kwamandan da ke kula da sashin Crack da ya gudanar da binke dangane da lamarin kuma da zaran an kammala bincike za a gurfanar dashi a gaban kotu domin ya suskanci shariya.
Comments
Post a Comment