Takaitattun labarain duniya daga shafin Al Nur hausa.

Takai tattun labarain duniya. Daga shafin Al Nur.
Bari mufara daga yanakin zirin Gaza yankin da kasar Israila ke baiwa hamata iska da falasdinawa. Ibrahim Alagha da shi da uwar gidansa sunkasance a Garin na Gaza ne domin su gudanar da hutunsu Amman sai akayi rashin sa a biyo bayan hare hare da jiragen yakin Israila ke kaiwa a yankin na zirin Gaza lamarin da ya sasu neman mafaka. Ma auratan biyu dai sun fitone daga wani gari da ake kira Irish tare da yaransu guda uku wanda kuma sunzo da sune domin su nuna musu garin su na asali kuma suga yan uwansu falasdinawa. Yana yin yaki da ake ciki yasa basu sadu da yan uwan nasuba sakamokon kai hare hare da kuma fashewar bamabumai a yankin na zirin Gaza.
A kasa Ghana kuwa wata matace mai suna Awusifa Kagbitor ta baiyana yadda ambaliyar ruwa yayi mata sanadiyar asaran kayakinta masu yawa. Tace tana zaune kwatsam sai taga ruwa yana malalowa daga tafki dake kusa da gidanta a tsakanin miti goma ruwa yayiwa gidanta kawaiya harma yaka mata wuya, bayan danda mai suna Kenneth yaji kuruwanta nan da nan ya taho domin ceton mahaifiyarsa. Matar yar shekaru 56 da haifuwa kuma manomiyace tana daya daga cikin dubbain mutane da ambaliyar ruwa ya shafa a yankin kudancin kasar Ghana.
A can kasar Venezuela kuwa hukumomin gwamnatin kasar ne da wakilain yan adawar kasar suka sanya hanu akan yarjejeniya da suka cimma domin ganin an gudanar da zaben ahugaban kasar da za ayi a kasar ta Venezuela. Gwamnatin kasar ta amince a gaiyato masu sanya ido na kasa da kasa da suzo su duba yadda za a gudanar da zaben wanda aka tsara za ayi a tsakiyar shekara ta 2024.
A kasar Iran kuma shugaban kasanne wato Ibrahim Raesi yace hare hare da Israila ke kaiwa Falasdinawa tana kashe wadanda baujiba ba suganiba musammanma mata da yara a Gaza. Shugaban kasan Iran Ibrahim Raesi ya baiyana hakane a lokacinda yake yiwa yan kasan Iran din jawabi. Inda ya kira dacewa Wannan rashi imanine da tausayi kuma ya baiyana cewa kasar Amurka tana goyon bayan Kasar ta Israila wajen kai hare hare.
Kucigaba da kasancewa da shafin Al Nur hausa domin karanta labarai da dumi duminsu daga sassan duniya daban daban. Baya ga shafin zaku samemu akan adireahinmu na yanan gizo wato WWW. labarunadamawa.blogspot.com. ko kuma Al nurblogspot.com. a koda yaushe kukeso.

Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

INTERNATIONAL HUMAN RIGHTS COMMISSION APPOINTS NEW LEADERS IN ADAMAWA STATE