Wadanda ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun shiga hanun runduna yan sandan jahar Adamawa.
N
Rundunan yan sanda a jahar Adamawa tayi nasaran cafke mutane shida da ake zargi da yin garkuwa da wani yaro dan shekara tara harma sun nemai kudin fansa na nera milyon biyar a cikin karamar hukumar Mubi ta kudu dake jahar Adamawa.
Wadanda ake zargindai dukkaninsu mazauna garin Mubi ne a anguwar Kaba dake kan titin zuwa karamar hukumar Maiha daga Karamar hukumar Mubi ta kudu. Wadanada ake zargi da yin garkuwa da yaron mai suna Mustafa Ibrahim a ranan 18-10-2023.
Kakakin rundunan yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Ngurojene ya sanar da haka a wata sanarwa da rabawa manema labarai a yola.
Sanarwan tace an samu nasaran cika hanu da wadanda ake zarginne biyo bayan koke da suka samu daga mahaifin yaron a ranan 19-10-2023 cewa wasu da ba asan ko siwayeba sun kutsa gidansa da aniyar sayan Zobo Juice inda sukayi awungaba da dansa mai shekaru sha tara.
Kawo yanzu dai kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya baiyana jindadinsa tare da yabawa DPO ofishin yan sanda dake Mubi tare da mutanensa bisa kokarinsu na ceto yaron daga hanun masu garkuwa da mutane.
Ya kuma bada tabbacin da zaran an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskaci shariya.
Comments
Post a Comment