Wani yaro ya rataye kansa a jahar Adamawa.
Rundunan yan sanda a jahar Adamawa tace ta samu rahoton cewa wani yaro ya rataye kansa a anguwar Runde Baru dake cikin karamar hukumar yola ta arewa a jahar Adamawa.
Kakakin rundunan yan sandan a jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya fitar a yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Sanarwan tace a yanzu haka rundunan tana aiki kafada da kafada da Jami an kiwon lafiya domin bankado musabbabin da yasa yaron ya rataye kansa.
Kwamishinan yan sandan jahar Adamawa Afolabi Babatola ya kirayi daukacin Al ummar jahar ta Adamawa da sukasance masu taimakawa rundunan da wasu bayanain sirri domi bata damar gudanar da aiyukanta yadda ya dace.
Comments
Post a Comment