AN TSARE WANI DA AKE ZARGI NARAWON MOTA NE TARE DA AIKATA ZAMBA.A JAHAR ADAMAWA.










Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta samu nasaran tsare Mubarak Andulkadiri mazaunin anguwar Shagari, dake cikin karamar hukumar Yola ta Kudu bisa zarginsa da aikata zamba dama satar mota.



Kakakin rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.



A ranan1-2-2025. Wani Mai suna Ahmed Salisu manajan wani Gidan Mai Mai suna Two Star dake Mubi ya shigar da korafin cewa Wanda ake zargin ya shiga Gidan Mai dinne tare da sayan Mai na dubu #97,850 tare da karban nera dubu 10,000 da sunan zai biya ta na uran POS, Yana Kuma tare da wata mota CRV Wanda ke dauke da rijistan number kasar waje HJ58URU.





Biyo bayan hakan  ne Jami an Yan sanda dake shelkwatan ofishin Yan sanda dake Mubi ta Arewa suka Kai daukin gaggawa inda suka tsare Wanda ake zargin a mashigar garin na Mubi, bisa bincike da aka gudanar Wanda ake zargi ya Gaza wajen bada cikekken bayani mallakar mota saboda ba wani shaidar takardan da ta nuna cewa motar tashice,.




Saboda haka rundunan Yan sandan a jahar Adamawa ta Mai sanar da jama a duk Wanda ya ke da shaidar mallakar motar Yana iyar ziyartan ofishin Yan sanda dake Mubi ko Kuma ya tuntuni kakakin rundunan Yan sandan jahar Adamawa domin Karin bayani.





Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT