GIDAN MAI MAI SUNA MRS FILLING STATION YA KAMA DA WUTA SAI DAI BA WANI RAHOTON ASARAN RAI.
Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta fara bincike gano musabbabin tashin gobara da ta faru a Gidan Mai na Mrs filling station, dake mahadar Bachure akan titin Numan lamarinda yafaru a Daren nan.
Jami in Hulda da jama a na rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nugoroje ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Bayan daukin gaggawa da rundunan ta Kai a inda lamarin ya faru. Ma aikata kwana kwana sun kawo karshen gobarar.
Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa CP Dankwambo Morris,psc(+), Yana Maraba da duk wasu bayanai da zasu taimaka wajen gudanar da bincike dangane da lamarin, tare da tabbatar da cewa rundunan tanan akan kafarta domin kare rayuka dama dukiyoyin Al umma a fadin jahar baki Daya.
Comments
Post a Comment