Kungiyar FOMWAN tayi kira ga
Gamayyar kungiyoyin mata musulmi ta yi kira da a aiwatar da tsarin da zai kawo karshen nuna wariya ga mata masu sanya hijabi.
An yi wannan kiran ne a yayin taron kungiyar mata musulmi ta FOMWAN da ke Yola, inda kungiyoyin mata musulmi suka taru domin tattauna batutuwan da suka shafi sanya hijabi da muhimmancinsa ta fuskar Musulunci.
A jawabin da ta gabatar, Hajiya A’ishatu Khamis ta jaddada muhimmancin sanya hijabi don kiyaye kyawawan dabi’u da kuma nuna kyawawan halaye na Musulunci.
Ta kuma bukaci mata musulmi da su yi riko da koyarwar Annabi Muhammad domin samun karbuwa a cikin al’umma.
Rukaiya Garba ta bayyana cewa taron ya ba da damar wayar da kan jama'a game da sanya hijabi a matsayin alama ta imani da sanin yakamata.
Amira na Kungiyar mata Musulmi wato FOMWAN Hajiya Khadija Buba ta ja hankalin iyaye da su rika umurtan Ya'yansu su sanya hijabi inda ta bayyana irin rawar da hakan ke takawa wajen kare su daga munanan halaye da kuma inganta tarbiyya.
Itama anata jawabin Fatima Ahmad Marafa ta bayyana muhimmancin taron, inda tace ya taimaka wa mahalarta taron su fahimci mahimmancin hijabi ta mahangar addinin Musulunci.
Comments
Post a Comment