Rundana Yan sandan jahar Adamawa ta lashi takwabin farauto wadanda sukayi garkuwa da shuwagabanin mujami u biyu a fadin jahar.





Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa CP Dankwambo Morris, yayi Allah wadai tare da nuna takaicinsa dangane da garkuwa da akayi da Rev. Father Mathew David Dusami na Mujami ar Katolic dake Yola da Rev. Father Abraham Samman na Jalingo, lamarin ya farune da asubahin Asabar 22-2-2025.



Kakakin rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.


Mamunan lamarin ya farune a gidansu dake Gwaids Malam a cikin karamar hukumar Numan a jahar Adamawa.




Masu garkuwa da mutanen dai sun kira kansu da sojoji dauke da mungan makamai sun Isa Gidan wadanda suajayi garkuwa da su da misalin karfe hudu na asuba 4:00. Sannan sukayi ayun gaba da su.




Kwamishinan Yan sanda Dankwambo Morris ya Sha alwaahin CETO mutanen saboda haka nema ya tura Jami an Yan sanda domin farauto masu garkuwa da mutane dama masu taimaka musu, tare Kuma da ceto wadanda akayi garkuwa da su ba tare da rauniba.




Rundunan Yan sandan tana iya kokarinta domin ganin ta cika hanu da masu garkuwa da mutane dama wadanda ke da hanu a cikin domin doka tayi aiki akansu.ya jaddada cewa rundunan a shirye take ta cigaba da kare rayuka dama dukiyoyin Al umma harma da dakile dukkanin aiyukan ta addanci a fadin jahar.




Garkuwa da shuwagabannin addinin abin bakin ciki ne Kuma baza a lamuntaba, saboda haka masu ruwa da tsaki dama jama a da suyi aiki tukuru domin Samar da zaman lafiya a tsakanin Al umma.



Don haka rundunan tana kira ga Al umma da sukasance suna baiwa rundunan hadin Kai da Kuma basu bayanain sirri akan lokaci Wanda hakan zai taimaka wajen Kai dauki da gaggawa tare Kuma da taikawa wajen ceto wadanda akayi garkuwa da su dama maka masu aikata laifuka.





Comments

Popular posts from this blog

Yola Zone: ASUU threatens to withdraw services on expiration of the 2-week ultimatum to FG

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT