An shawarci manoma da kada suyi saurin sayar da kayakin da suka noma.
Daga Alhassan Haladu Yola.
A yayinda ake cigaba da girbe amfani gonna an kirayi manoma da sukasance suna yin kaffa kaffa wajen sayar da amincin da suka noma domin kaucewa shiga wahala.
Alhaji Usman Suleiman Pallam Kuma kwarerren ne a harkan noma shi ya bada wannan shara a zantawarsa da manema labarai a Yola a fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Alhaji Usman Suleiman yace faidar gaggauta sayar da kayakin noma kadanne saboda haka bai Kamata manomi ya gaggauta sayar da kayakin da ya nomaba, ya dan Jira kadan saboda kayakin ya dan Kara farashi duba da yadda aka Samu tsadar kayakin aikin noma da tsada Lamar su taki maganin feshi da dai sauransu.
Usman Suleiman Pallam ya koka da yadda manoma suka fuskanci wahala da tsadar kayakin noma, saboda haka Yana da muhimmanci manoma su kasance suna taka tsantsan wajen sayar da amfanin gonakainsu.
Dangane da ajiya kuwa, Pallam yace akwai dabaru daban daban da za ayi amfani da su wajen yin ajiya ba lallene sai anyi amfani da sanadireba wand zaiyiwa Al umma illa, saboda haka ya Kamata a kaucewa yin amfani da sanadari wajen aniyar kayakin abinci.
Ya Kuma kirayi manoma da kada suyi kasa a gwiwa wajen gudanar da harkokin noma domin a cewarsa yin noma yafi raahinyi saboda haka manoma sukara himma wajen yin noma.

Comments
Post a Comment