CP ADAMAWA YA UMURCI A GAGGAUTA FARA BINCIKE KAN ZARGIN WANI FASHI DA MAKAMI A WANI GIDA DAKE NGURORE, YOLA KUDU
Daga Alhassan Haladu Yola.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Adamawa, CP Dankombo Morris, Psc(+), ya bayar da umarnin da a gaggauta fara bincike kan wani zargin fashi da makami a Wani gida da ake cewa ta faru a gidan wani matashi mai shekaru 25, Akwarakiram Abel, mai aiki da POS, da ke Sabon Pegi a Ngurore, Karamar Hukumar Yola ta Kudu.
Kakakin Rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ne ya Sanar da haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Yola.
Hakan na zuwa ne bayan korafin da iyalan matashin suka kai cewa a safiyar 21 ga Nuwamba, 2025, tsakanin karfe 3:00 na dare zuwa 4:00, wasu da ba a san su ba, dauke da makamai, suka kutsa gidan, suka farmake shi tare da kwace masa kayansa. A cewar rahoton, ‘yan fashin sun yi masa mummunan rauni da adda, abin da har ya kai ga yanke masa hannu.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa za a gudanar da bincike mai zurfi don cafke wadanda suka aikata laifin tare da tabbatar da an yi adalci ba tare da bata lokaci ba.
Rundunar ta kuma tabbatar da aniyar ta na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da ba da hadin kai don tabbatar da tsaro.

Comments
Post a Comment