Kamfanin Sugar na Dangote na karfafa zamanta kewa da al'umma ta hanyar ganawa da masu ruwa da tsaki







Babangida Galleon 



Kamfanin sugar na Dangote dake Numan ta jaddada anniyarta na ci gaba da tattaunawa da al'umma dake kewaye da ita domin karfafa zaman lafiya da ke tsakanin su.


 Manajan sashin ganawa da masu ruwa da tsaki na kamfanin, Malam Bello Danmusa ne ya baiyana haka yayin zaman ganawa da masu ruwa da tsaki da aka yi a garin Numan.



Manajan Sashin ganawa da masu ruwa da tsaki, Malam Bello Danmusa  yace makasudin wannan zaman tattaunawar dai, wanda kamfanin ta assasa  shine domin  ganawa da shugabannin al'umma, na gargajiya, shugabannin mata da matasa da ma duk wadanda suka kamata.



Danmusa yace ana samun nasarori sakamakon ganawar da ake yi bayan watanni uku, ganin yanzu kamfanin ta yi nasarar shawo kan matsalar tsaro da take fama da shi sakamakon haɗin kan da take sanu daga al'umma.


 

Yace za a ci gaba da ganawar domin samar da dandalin zaman lafiya tsakanin kamfanin da al'umma dake kewaye da ita.



Ya kuma yaba tare da kira gare su dai su ci gaba da baiwa kamfanin haɗun kai domin ci gaban bangarorin biyu.



Hakikin Gyawana, Chief Agoso Bamaiyi yayi bayani cewa zama da kamfanin , wanda ɗaya ne daga cikin manyan masu taka rawa a harkar tattling arziii a jahar  ya samar da dama da dukkan bangarorin za su tattauna matsaloli da ake fama dasu , da ma mafita.



Hakimin ya kirayi kamfanin da ta ci gaba da shirin ta na bada tallafi dama na noma, ganin suna da muhimmanci gurin  karfafa harkokin tattling arzikin wadannan al'umma.



Haka shima jagoran matasan kauyen Dubon,  Justin Zakari,  da Jennifer Hanson daga kauyen kawon sun tabbatar da cewa mu'amala tsakanin kamfanin Dangote da al'umma da ke kewaye da ita na da kyau, ganin ana samun tallafin karatu, talladin sana'oi, gine gine da dai sauran su.



A jawabin shi, shigaban sashin hulda da al'umma na kafabin, Daniel Andrew yace makasudin wannan zama dai shine ganawa da masu ruwa da tsaki,  a kuma tattauna hanyotin da za su kawo wa bangarorin biyu ci gaba.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

TSARO: AN BUKACI YAN NAJERIYA SUKASANCE MASU BAIWA HUKUMOMIN TSARO HADIN KAI DA GOYON BAYA.

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT