Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa, ASUU reshen Yola, ta zargi gwamnati da sakaci kan ilimin jami’a
Daga Alhassan Haladu Yola.
Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa, ASUU, reshen Yola, ta nuna damuwa kan abin da ta kira rashin niyyar gwamnatin tarayya wajen magance matsalolin da suka daɗe suna damun jami’o’in gwamnati.
Hakan na kunhene a cikin wata sanarwa dauke da Sanya hanun Ko odinatan kunguyar ASUU dake shiyar Yola Dani Mamman
Shiyyar Yola — wadda ta haɗa da jami’o’in ADSU Mubi, BOSU Maiduguri, FUGA Gashua, MAU Yola, TSU Jalingo, UNIMAID da YSU Damaturu — ta bayyana haka yayin wani taron manema labarai ranar Litinin.
ASUU ta ce gwamnati na nuna rashin gaskiya da ƙara sakaci a tattaunawar da ake yi kan yarjejeniyarsu, duk da cewa ƙungiyar ta dakatar da yajin-aikin gargadi ne domin ba wa tattaunawa dama, bayan roƙon dalibai, iyaye da masu ruwa da tsaki.
Kungiyar ta ce duk da cewa ta yi wa gwamnati wata guda don kammala yarjejeniyar, kwanaki biyu kacal bayan janye yajin aiki, ya bayyana cewa gwamnati ba ta da niyyar cin gajiyar damar.
ASUU ta yi zargin cewa gwamnati tana kallon ilimi a matsayin sana’ar kasuwa, tana mai cewa ƙarin albashin da ake shawarar bayarwa bai dace ba, kuma ba zai hana ƙauracewar ƙwararru daga jami’o’i ba.
Ta ce duk da ɗan ci gaban da ake magana akai a batutuwan da ba na kuɗi ba, albashi da jin daɗin ma’aikata na nan a mataki mai rauni. ASUU ta kuma ƙalubalanci ikirarin gwamnati na cewa ba kuɗi, tana mai jaddada cewa abin da ke babu shi shi ne kyakkyawar manufa.
Shiyyar Yola ta ce watanni masu yawa an ga ƙaruwa a rabon kuɗin gwamnati daga Asusun Tarayya, tana mai jan kunne cewa jinkirin ƙare tattaunawar na iya jefa jami’o’i cikin wani sabon rikici.
Kungiyar ta roƙi shugabanni na gargajiya, dalibai, iyaye, ƙungiyoyin farar hula da NLC su matsa wa gwamnati lamba don daukar mataki cikin gaggawa.
ASUU ta ce malamai sun cancanci albashin da ya dace, dalibai kuma sun cancanci ilimi ba tare da tangarɗa ba, tana gargadin cewa kasa da ta yi watsi da malamanta “ta buɗe wa kanta rami.”

Comments
Post a Comment