PPSMB. TA RARRABA KAYAKIN KARATU A MAKARANTUN GABA DA FIRAMARE DAKE FADIN JAHAR ADAMAWA.

 








Daga Alhassan Haladu Yola.


A kokarin bunkasa ilimi a jahar Adamawa, Hukumar dame kula da makarantu gaba da firamare a jahar Adamawa ta rarranawa makarantu gaba da firamare kayakin karatu a dukkanin makarantu dake fadin jahar Adamawa.


Rarraba  kayakin ya gudanar a harabar shelkwatan Hukumar dake dake Yola.


Da yake Mika kayakin ga shuwagabanin makarantu gaba da firamare, Babban sakataren  riko Hukumar dake kula da makarantu gaba da firamare a jahar Adamawa Mr Butsan Penuel ya baiyana godiyarsa ga Allah madaukakin sarki tare da godewa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, Wanda da yardansa da amincewarsa ne suka Samu daman rarraba wannan kayakin karatun ga makarantu gaba da firamare dake fadin jahar baki Daya.




Mr Birssn Penuel yace sun rarraba kayakin ne domin ganin an Samu cigaban ilimi a tsakanin dalube dake fadin jahar, a Wani mataki na bunkasa ilimi a fadin jahar ta Adamawa.



Mr Birsan ya Kuma kirayi shuwagabanin makarantu gaba da firamare dake fadin jahar da su Maida hankali sosai wajen yin amfani da kayakin da suka Karba ta yanyar da ta dace domin Samu cigaban da Kuma Samu nasaran inganta ilimi.




Ya shawarci iyaye da Suma su Bada tasu gudumawan wajen tura yaransu makarantu akan lokaci domin yaran su Samu damar yin karatu yadda ya Kanata domin su Samu nasaran cin jaranawa.




Wasu daga cokin shuwagabani makarantu sun baiyana farina cikinsu da Jin dadinsu dangane da kayakin da aka raba musu tare dayin alkawarin yin amfani da kayakin yadda ya Kanata domin Samun cigaban ilimi yadda ya Kanata a fadin jahar.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT