Rundunan Yan sandan jahar Adamawa ta ceto yaran mata biyu wadanda akayi yunkurin safaransu zuwa kasar Ghana.






Daga Alhassan Haladu Yola.


Rundunan Yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran kama Wanda ake zargi da safaran mutane.tare da ceto mata biyu wadanda akayi aniyar safaransu.




A kokarinta na yaki da safaran mutane dama aikata laifuka  rundunan Yan sandan jahar Adamawa tayi nasaran dakile aiyukan safaran mutane.


Kayakin rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje me ya Samar da haka a wata sanarwa da yaranawa manema labarai a Yola.




A ranan 12 -11-2025 rundunan ta sashin tattara bayanai sirri dake Nan Yola. Biyo bayan bayanai sirri da ta Samu Wanda hakan yakaita da Samun nasaran tsare Wani mai suna Hamza Hammantukur  Isa mai shekaru 40 da haifuwa Kuma mazaunin a titin Bauchi dake cikin karamar Hukumar Yola ta Arewa, Wanda ake zargi ya kware wajen yin safaran yaran mata daga Adamawa zuwa Ghana domin sasu yin karuwanci, Kuma Yana yaudaransune ta Samar musu da aiki, da zasu Samu kudi mai yawa.




A lokaci aka gudanar da sintiri dangane da lamaein an ceto yaran mata biyu masu shekaru daga 18 da 19 Kuma an ceto su batare da Jin rauniba.




A binciken farko da aka gudanar dai ya nuna cewa Wanda ake zargi Yana gudanar da wannan aiki tun daga shekara ta 2023 Kuma tunin ya amsa laifinsa harma yace yanzu haka akwai yaran mata 10 da yayi safaransu zuwa Ghana tare da hadin kan wasu mata biyu.




Kawo yanzu dai rundunan na iya kokarinta domin kama wadanda suke taimaka masa tare da gudanar da binciken domin ceto yaran da akayi safaransu.




KWamishinan Yan sandan jahar Adamawa CP Dankwambo Morris ya yabawa shugaban  sashin tattara bayanain sirri tare da mutanensa bisa daukan mataki da sukayi akan lokaci. Ya Kuma tabbatar da cewa rundunan a ahirye take ta kare rayuka dukkanin mazauna jahar ya Kara da cewa da zaran an kammala binciken za a gurfanar da Wanda ake zargi gaban kotu domin ya fuskanci shariya.




Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT