WASU MANOMA SUN MAIDA HANKALI WAJEN NOMA IRI A JAHAR ADAMAWA.

 








Daga Alhassan Haladu Yola.



A Wani mataki na bunkasa harkokin noma a fadin Najeriya wasu manoma a jahar Adamawa sun rugumin harkan noma inganceccen iri domin sayarwa manoma iri da zasu shuka a gonakainsu domin Samar da wadaceccen abinci a tsakanin Al imma.


A zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa shugaban kungiyar manoma iri a jahar Adamawa Alhaji Baba Sahabo yace sun dauki matakin shiga harkan noma iri ne duba da yadda ake fuskantar sauyin yanayi a bangaren harkokin noma wadanda suka hada da Samun jinkirin damina, ko daukewar damina da wuri, fari da dai sauransu.


Alhaji Baba Sahabo yace bayan sun Samu horo na ahekaru biyar, Wanda hakan ya Basu damar Maida hankali wajen noma iri  da zai dai dai da kowane  yanayi domin Samun damar bunkasa harkokin noma a jahar da ma kasa baki Daya.



Da yake baiyana dalilinsu na shiga harkokin noma iri. Alhaji Sahabo yace sun dauki matakin hakane saboda yadda manoma ke shiga wahala wajen Samun inganceccen iri da zasu shuka Wanda zai Basu abinci mai yawa saboda haka su ka ga ya Kamata su sauwakawa manoma domin ganin sun bunkasa aiyukansu yadda ya Kamata.



Alhaji Baba yace kawo yanzu sun Samu cigaba sosai, Wanda acewarsa suna noma kadada da dama na iri a cikin kananan hukumomi takwas dake jahar Adamawa, Wanda a yanzu haka suna so su fadadashi zuwa kananan hukumomi 21 dake fadin jahar ta Adamawa baki Daya.



Ya Kuma baiyana cewa suna fuskantar kalubale da dama da suka hada da tsadar da taki keyi da kayakin feshi da dai sauransu, saboda haka nema suke Kiran gwamnatin tarayya Dana jihohi, harma Dana kananan hukumomi da sukasance suna taimakawa manoma ko masu rangwame a kayakin noma Wanda hakan zai taimaka musu wajen inganta aiyukansu na noma.




Ya Kara da cewa Yana ya kinin cewa in har suna Samun kayakin noma a cikin farashi mai rahusa to da yardan Allah baza a ahigo da kwayar abinci ko Daya daga kasashen wajeba, saboda haka suna bukatan goyon bayan sosai daga dukkanin gwamnatocin.


Da wannan yake Kira ga daukacin manoma a Najeriya da sukasance sun Maida hankali wajen Neman inganceccen iri da zasu shuka a gonakainsu, da Kuma rungumar noma a zamunance domin Samar da wadaceccen abinci a fadin Najeriya.


Ya Kuma kirayi matasa a fadin Najeriya da su shiga harkokin noma domin Wanda a cewarsa noma zai ciresu daga kangin talauci da Kuma Samar musu da aikinyi a tsakanin Al imma.

Comments

Popular posts from this blog

ASUU MODIBBO ADAMA UNIVERSITY BRANCH COMMENCED TWO WEEK WARNING STRIKE.

Breaking News: Muhammad Ahmad Song (Boboi/Baka)Passes Away at 83

ADAMAWA APEX CHOICE MOST INFLUENTIAL WOMEN IN ADAMAWA AWARD NIGHT