Gwamna Fintiri na jahar Adamawa Ya Gargadi Jami’an Kula da Daji Kan Yin Aiki Cikin Kwarewa
Daga Ibrahim Abubakar Yola.
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya gargadi sabbin jami’an kula da daji (Forest Guards) da aka horar da su da su gudanar da ayyukansu cikin kwarewa tare da gujewa tsoratarwa ko cin zarafin ‘yan kasa masu zaman lafiya.
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a yayin bikin kammala horas da jami’an kula da daji guda 987 da aka gudanar a Kwalejin General Murtala Mohammed (GMMC), Yola. Mataimakiyarsa, Farfesa Kaletapwa George Farauta, ce ta wakilce shi a wajen taron.
Gwamna Fintiri ya shawarci wadanda suka kammala horon da su dauki kansu a matsayin ‘yan kasa na musamman da aka zaba domin yi wa al’ummominsu da kasa hidima, yana mai jaddada cewa horon da suka samu ya kamata a yi amfani da shi wajen kare rayuka, dukiyoyi da muhalli, ba wai wajen cin zarafin iko ba.
Farfesa Farauta ta yabawa Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) bisa rawar da ya taka wajen tsarawa da sa ido kan shirin jami’an kula da daji, tana mai bayyana shirin a matsayin muhimmin bangare na yaki da matsalolin tsaro da ke da alaka da yankunan dazuka.
Ta kuma bukaci jama’a da su ba da hadin kai da goyon baya ga jami’an kula da daji da aka tura zuwa al’ummominsu, tana mai cewa hadin kan al’umma yana da matukar muhimmanci wajen samun nasarar shirin.
Gwamnan ya sake jaddada kudurin Gwamnatin Jihar Adamawa na ci gaba da tallafa wa wannan shiri.
“Ni kuma, ina so in tabbatar muku da ci gaba da goyon bayan Gwamnatin Jihar Adamawa ga wannan shiri,” in ji shi, yana kuma addu’ar samun dorewar zaman lafiya da tsaro a Jihar Adamawa, Najeriya da ma duniya baki daya.
Tun da farko, Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya ce shirin jami’an kula da daji yana hade kare muhalli da manufofin tsaron kasa.
“Ta hanyar kare dazuka, muna dawo da yankunanmu. Ta hanyar dawo da yankunanmu, muna kare al’ummarmu da makomarsu,” in ji Ribadu.
Wanda Kanar E. E. Eswagu ya wakilta, NSA ya tabbatar da kudurin ofishinsa na ganin shirin ya yi nasara, yana mai tabbatar wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu aniyarsu ta samar da sakamako mai ma’ana a bangaren tsaro, muhalli da tattalin arziki, bisa tsarin Renewed Hope Agenda.
Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro ya kuma sanar da fara biyan albashi da alawus-alawus nan take, tare da gaggauta tura sabbin jami’an kula da daji bakin aiki domin kara kwarewa da kwarin gwiwa.
Daukar jami’an kula da daji ya biyo bayan ayyana dokar ta-baci kan tsaro a fadin kasa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi, wadda ta hada da umarnin daukar karin jami’an soja da ‘yan sanda domin karfafa tsaro a duk fadin Najeriya.

Comments
Post a Comment