KUNGIYAR MAFARAUTA TASHA ALWASHIN WANZAR DA ZAMAN LAFIYA A FADIN NAJERIYA.
Daga Alhassan Haladu Yola.
Yayinda ake daf da shiga sabuwar shekera ta 2026 an kirayi Al umma da su cigaba da baiwa hukumomin tsaro da Mafarauta hadin Kai da goyon baya domin ganin an Kai ga Samun nasaran dakile matsalar kalubalen tsaro a fadin Najeriya.
Shugaban kungiyar Mafarauta a Najeriya a yankin arewa masau gabas Modibbo Idris Usman Tola ne yayi wannan Kira a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.
Modibbo Idris Usman Tola yace Yana da muhimmanci Yan Najeriya sukasance a Koda yaushe suna taimakawa jami an tsaro, Wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen magance matsalar tsaro baki Daya.
Modibbo Idris yace duk da cewa gwamnatin jahar Adamawa tana iya kokarinta wajen tsaro Amma Yana Kara Kira a gareta dama masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro da su taimakawa Mafarauta da issassun kayakin aiki da zasu taimaka wajen dakile aikata laifuka a tsakanin Al umma.
A cewar Modibbo dai Mafarauta na Samun karancin kayakin aiki don haka ya Kamata a taimaka masu da wadadattun kayakin aiki da zai basu damar gudanar da aiyukansu yadda ya Kamata.
Modibbo ya tabbatar da cewa kungiyarsu a shirye take ta baiwa jama a kariya domin Samar da zaman lafiya a fadin Najeriya baki Daya. Domin a cewarsa Mafarauta suna taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa hukumomin tsaro.
Ya Kuma yabawa gwamnatin jahar Adamawa karkaahin jagorancin gwamna Ahmadu Umaru Fintiri dangane da yadda ya inganta tsaro a fadin jahar Adamaww.

Comments
Post a Comment