Arewa Traders Association ta jajantawa gwamnatin jahar Kano dama iyalen marigayi Bature AbdulAziz Wanda Allah yayiwa Rasuwar a jahar Kano.
Daga Alhassan Haladu Yola.
Kungiyar Yan kasuwa dake Yankin Arewacin Najeriya wato Arewa Traders Association of Nigeria, tana mai Mika ta a aziyarta ga gwamnatin jahar Kano, da daukacin Al ummar jahar Kano da daukacin Yan kasuwar Arewacin Najeriya, Dana kasa harma da iyalen marigayi Alhaji Bature AbdulAziz bisa Rasuwar Alhaji Bature AbdulAziz. shugaban Yan kasuwa Najeriya Kuma shugaban kwamitin amintattu wato BOT na Arewa Traders Association.
Shugaban kungiyar Yan kasuwa na yankin Arewacin Najeriya wato Arewa Traders Association, Alhaji Muhammed Ibrahim 86 ne ya baiyana haka a sakonsa na ta aziyar da aka rabawa manema labarai a Yola.
Alhaji Muhammed Ibrahim yace kungiyar tasu ta kadu kwarai da Jin labarin Rasuwar Bature INDA ya baiyana rashin marigayi a matsayin Babban Rashi ba ga Al ummar jahar Kano ba har da Yan kasuwa dama kasa baki Daya.
Sanarwa ta Kara da cewa kingiyar tana mai Mika jajenta ga gwamnatin jahar dama iyalen marigayi tare da Yi masa Adu ar Allah madaukakin sarkin ya gafarta masa ya Kuma jikanshi yasa Aljannace makomarsa.
Alhaji Ibrahim ya Kuma Yi Adu ar Allah ya baiwa iyalensa jimre hakurin Rashi da sukayi Wanda a cewarsa Basu kadai sukayi rashiba lamarin ya shafi kungiyar Yan kasu dake Arewacin Najeriya.
Alhaji Bature AbdulAziz dai ya rasune a Kano sakomokon gajeruwar rashin lafiya da yayi fama da ita, Kuma tunin akayi Jana izarsa Lamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Comments
Post a Comment