Kamfanin Sugar na Dangote ta inganta harkar ilimi ta hanyar samar da kyakkyawar yanayin ɗaukar darrussa a yankin Numan
Daga Babangida Galleon
Kamfanin Sugar na Dangote dake Numan ta tallafawa makarantar jeka da dawo dake yankin Ngbalang da kujerun karatu a kokarin ta na dafa wa gwamnatin jaha gurin inganta harkar ilimi a faɗin jahar.
A jawabin da yayiwa manema labaru jim kadan bayan mika waɗannan kujeru wanda aka yi a harabar makarantar, shugaban sashin kula da ma'aikata na kamfanin, Mista Moses Joash yace daukan wannan mataki na kumshe cikin tsarin tafiyar da kamfanin a bangaren karfafa harkar ilimi a cikin al'ummomi dake kewaye da ita.
Shugaban sashin kula da ma'aikatan , Mista Moses Joash
Yayi bayanin cewa bada wannan tallafi ya zamo tilas ganin muradin kamfanin ne baiwa ilimi fifiko, musamman na yara manyan gobe.
Moses ya bada tabbacin cewa kamfanin zata ci gaba yin iya kokarin ta gurin bada gudummowa domin ci gaban wadannan al'ummomi dake kewaye da ita.
Shugaban makarantar, Malam Suleiman Abbas wanda ya amshi kujerun a madadin makarantar ya godewa kamfanin Dangote da wannan kokarin, lamarin da yace zai taimaka matuka a bangaren malamai da ma daliban baki daya.
Sakataren ma'aikatar ilimi na karamar hukumar Numan
Kwamaret Patrick Bauti, wands har wa yau shi ya wakilci shugaban karamar hukuma ya godewa kamfanin sugar na Dangote da bada wannan gudummowa, inda ya bada tabbacin kula da kuma adanan su.
A nasu jawabin, hakimin yankin Imburu wanda ya wakilci masarautar kasar Bachama, da sauran masu ruwa da tsaki sun mika sakonnin godiga da jinjina wa kamfanin Dangote da yadda take ci gaba da tainakawa a bangaren ilimi da ma sauran bangarorin, tare da bada tabbacin bata goyon bayan su a ko da yaushe.
Abubuwa da suka wakana yayin bukin sun hada da rawan gargajiya daga ɗaliban makarantar.

Comments
Post a Comment