Ma aikatar harkokin noma a jahar Adamawa ta kudiri aniyar dakle cututtuka dake ciwa manoma tuwo a kwarya a fadin jahar Adamawa.
Daga Alhassan Haladu Yola.
A kokarinta na inganta harkokin noma a fadin jahar Adamawa, Ma aikatar harkokin noma a jahar Adamawa ta shirya Taron Karawa juna sani wa manyan jami an ma aikatar dake kananan hukumomi 21 dake fadin jahar dangane da yadda za a magance dukkanin cututtuka dake addabar anfanin ganakai a fadin jahar.
Taron Karawa Juna sani na kwanta Daya ya gudana ne a ma aikatar harkokin noma dake sakatariya gwamnatin jahar Adamawa.
Da yake yiwa ma halarta Taron jawabi kwamishinan harkokin noma a jahar Adamawa Fafesa David Katau bayan ya marabci mahalarta Taron ya yabawa Babban sakatariya dake ma aikatar dama sashin kula da aiyukan noma bisa shiraya wannan taro tare da Kiran mahalarta da suyi anfani da abinda aka koya musu domin Samun cigaban harkokin noma a jahar Adamawa.
Kwamishinan ya Kuma shawarcesu da su fadada fadakarwa dangane da cututtuka dake addabar ganokai zuwa yankunan karkara domin ganin an dakile matsalar cututtuka a gonakai.
Dangane da sabbin ma aikatar da aka dauka kuwa kwamishin ya kirayi jami an da sukasance masu koyawa sabbin ma aikatan aiki Wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa harkokin noma a jahar Adamawa.
Farfesa Jatau ya yabawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa kokarinsa na Maida hankali tare da taimakawa ma aikatar noma wajen inganta tare bunkasa harkokin noma a jahar Adamawa.
Shima a jawabinsa Dr Ibrahim Bayaso wandama shine ya jagorancin Taron yace sun shirya Taron bitan ne domin fadakar da Jami an ma aikatar gona kan yadda ake Samun bullar cututtuka a ganakai, saboda haka ne aka ga ya Kamata a wayarwa Al umma Kai musammanma monama dangane da abinda a shafi cututtuka,
Dr Ibrahim Bayaso Shima ya shawarci mahalarta Taron da suyi anfani da ilimin da suka Samu wajen bunkasa harkokin noma a fadin jahar Adamawa.
Wasu daga ckin mahalarta Taron sun baiyana farina cikinsu dangane da wannan taro da aka shirya musu sun Kuma tabbatar da cewa zasuyi amfani. da ilimin da suka koya yadda ya Kamata domin inganta harkokin noma a fadin jahar.

Comments
Post a Comment