Ma aikatar ilimi a jahar Adamawa ta rarranawa manyan makarantu sakandare dake fadin jahar.
Daga Alhassan Haladu Yola.
Gwamnatin jahar Adamawa ta ma aikatar ilimi ta rarranawa daukacin manyan makarantu sakandare dake fadin jahar Adamawa takardun karatu a Wani mataki na bunkasa ilimi a fadin jahar Adamawa.
An dai rarraba takardun ne a makarantar kwalejin tunawa da General Murtala Muhammed dake Yola a jahar Adamawa.
Da yake jawabi a yayin kaddamar da rarraba takardun kwamishinan ilimi dake jahar Adamawa Dr Garba Pella yace wannan rarraba takardun Yana daga cikin aniyar gwamnati in inganta tare da bunkasa ilimi a tsakanin dalube dake fadin jahar Adamawa.
Dr Garba Pella yaja hankalin shuwagabanin makarantu da su Maida hankali sosai wajen kula da kayakin da aka basu Wanda hakan zai taimaka wajen baiwa Yara ilimi da ya Kamata.
Ya Kuma sake jaddada aninyar gwamnatin nayin dukkanin abinda suka dace domin ganin dukkanin dalube sunyi sanaran cin jarabawar kammaka sakandare da sakamoko mai kyau don haka gwamnati ta kimtsa tsaf domin ganin an baiwa Yara ilimi kyauta a fadin jahar.
Da yake nashi jawabi Babban sakataren hukumar dake kuka da makarantu gaba da firamare PPSMB a jahar Adamawa Mr Birsan Peniel ya jaddada kiran shuwagabanin makarantu da su kula da takardun da aka basu, Kuma su nisanta kansu da sayar takardun domin a cewarsa duk Wanda aka Samu Yana kokarin sayar da takardun to yayi kuka da Kansa, domin za a lamunce da haka ba.
Mr Birsan Penuel ya shawarci shuwagabanin makarantu da sukasance masu hada kansu da Al ummomin dake yankinau wajen baiwa makarantu tsaro da yakamata domin dalube su Samu sukunin karatu na tare da fargaba ba.
Ya Kuma kirayi daukacin malamai da Suma sukasance masu anfani da takardun yadda ya dace da Kuma su jajirce wajen karantar da Yara domin ganin an Samu cigaban ilimi a fadin jahar ta Adamawa.
Mr Birsan ya Kuma shawarci iyaye da Suma su bada tasu gudumawar wajen taimakawa malamai dama makarantu harma da tura yaransu a makarantu akan lokaci domin a cewarsa hakan ne zai baiwa malamai kwarin gwiwa karantar da yaran yadda ya Kamata.
Harwayau Mr Penuel ya baiyana cewa gwamnatin tana biyan kudaden jarabawan kammala sakandare dama bda ilimi kyauta saboda haka baiga dalili da zaisa iyaye baza su tura yaransu makarantu a.
Saboda haka yaja hankalin malamai da iyaye sukasance masu hada kansu a Koda yaushe da Kuma tuntuban juna Akai Akai Wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen inganta karatun yaran yadda Kamata.
Ya Kuma yabawa gwamna Ahmadu Umaru Fintiri bisa kokarinsa na baiwa bangaren ilimi fifiko da Kuma yadda yake rarrawa makarantu kayakin karatu da dai sauramsu domin cigaban Al ummar jahar baiki Daya.
Itama a nata bangaren Babbar sakatariya a ma aikatar ilimi dake jahar Adamawa Hajiya Aisha Muhammed Umar Kira yayiwa shuwagabanin makarantu da sukasance masu Sanya Ido akan takardun domin ganin Basu lalaceba Kuma anyi anfani dasu yadda yakamata.
Ta Kuma shawarci dalube dake fadin jahar Adamawa da su Maida hankali wajen karatunsu yadda ya Kamata domin ganin sun Samu nasaran kammala makarantar ba tare da wata matsalaba. Wanda Kuma hakan ne zai basu damar Samun sakamoko mai kyau.
Cikin takardu da aka rarraba dai sun hada da , biology, chemistry, mathematics da dai sauramsu.

Comments
Post a Comment