An bukaci Al umma da su dukufa wajen taimakawa marayu.
An kirayi Al ummah musamanma mawadata da sukasance masu taimakawa marayu a fannoni daban daban domin Suma su samu walwala a tsakanin Jama a. Shugaban makarantar Al IMAN Hajiya Amina Shuaibu ce tayi wannan kira a lokacinda da dake jawabi da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa. Hajiya Amina Shuaibu tace taimakawa marayu abune da yake da mutukan muhimmanci saboda haka Yana da muhimmanci Al ummah su Kara himma wajen taimakawa marayu domin rage musu radadin yanayi da suke ciki. Hajiya Amina tace makarantarta ta Al IMAN makarantace da ta maida hankali wajen tallafawa marayu musamma a bagaren basu ilimi Wanda Kuma kawo yanzu makarantar ya karantar da marayu da dama. Saboda haka ana iya daukan nauyin marayu domin karantar dasu a makarantu Wanda hakanma zai taimaka wajen inganta rayuwar marayun a Koda yaushe. Saboda haka akwai bukatar mawaadata sun tashi tsaye domin tallafawa marayu ta fannoni daban daban.