An bukaci da direbobi su Maida hankali wajen tuka motoci su a Koda yaushe.
By Alhassan Haladu Yola.
Domin ganin an Samu nasaran kare rayuka da dukiyiyin matafiya an kirayi direboji da su kaucewa diban fasinjoji da kaya fiye da kima dama dai yawan gudu da dai sauransu domin Samun cigaban aiyukansu yadda ya Kamata.
Kwamishinan Yan sandan jahar Adamawa Kabir Umar Hassan ne yayi wannan Kira a lokacin da yake jawabi a gangamin wayarwa direbobi Kai a Babbar tashar motoci dake Jambutu a karamar Hukumar Yola ta arewa a jahar Adamawa.
Kwamishinan yace sun dauki matakin shirya gangamin ne domin ganin an kare rayuka dama dukiyiyin matafiya a dukkanin hanyoyi dake fadin Najeriya, Wanda a cewarsa hakan zai kawo cigaba yadda ya Kamata.
Kwamishin ya shawarci direbobin da su Maida hankalin wajen gudanar da aiyukansu da Kuma yin tuki a tsanake cikin kwanciyar hankali domin tsira da rayukan fasinjoji da Kuma raguwar Samun hatsari.
Ya kirayi direbobin da a Koda yaushe sukasance masu bin ka idojin tuki dama dokokin kan hanya Wanda hakan zai taimaka wajen kariya daga Samun hatsari akan hanyoyi.
Da yake nashi jawabi shugaban a kungiyar direbobin wato N U R T W dake Babbar tashar motoci a Jambutu Malam Suleiman Hassan ya baiyana godiyarsu ha rundunan Yan sanda dangane da shirya wannan gangami da sukayiwa direbobi, Wanda hakan zai taimaka wajen inganta aiyukansu yadda ya Kamata.
Ya Kuma tabbatar da cewa zasuyi dukkanin maiyiwa domin ganin direbobin sunbi dukkanin ka idojin tuki dama dokokin kan hanya domin ganin an Samu nasara wajen raguwar hatsari a kan hanyoyi dake fadin Najeriya.
Daga bisani dai rundunan Yan sandan ta ziyarci sakatariyar Jam iyun siyasa wadanda suka hada da A P C, A D C, P D P, inda kakakin Rundunan Yan sandan jahar Adamawa SP Suleiman Yahaya Nguroje ya ja hankalin matasa da su kaucewa dukkanin abinda zai kawo tashin hankali musammanma a lokacin zabe dake tafe.
Ya shawarci matasan da Suma su Bada tasu gudamawan wajen Samar da zaman lafiya da hadin Kai a tsakanin Al umma domin samu cigaba yadda ya Kamata.
Shirya wannan gangami dai na zuwane a yayinda ake daf da gudanar da bikin ranan Yan sanda ta kasa na shekara ta 2026 mai taken hada Kai da Al umma domin Gina gaskiya.

Comments
Post a Comment