Ma aikatar harkokin noma a jahar Adamawa ta dauki matakin dakile kalubale dake fuskantar manoma domin Samar da wadaceccen abinci.
Daga Alhassan Haladu Yola. Ma aikatar harkokin noma a jahar Adamawa ta dauki matakin magance matsaloli da manoma ke fuskanta wadanda suka hada da rashin Samun inganceccen maganin feshi, dama iri da da dai sauransu. Kwamishinan harkokin noma a jahar Adamawa Farfesa David Jatau ne ya baiyana haka a lokacin yake jawabi a wurin Taron tattaunawa da masu ruwa da tsaka akan harkokin noma dama hukumomin tsaro da ma sauran hukumomi Wanda ya gudanar a sakatariyar gwamnatin dake Yola. Kwamishinan Wanda Babbar sakatariyar a ma aikatar harkokin noma a jahar Adamawa Mrs Heidi E Sunday ta wakilta tace sun taru da masu ruwa da tsaki ne wadanda suka hada da masu sayar da magunguna feshi, manoma, hukumomi, harma da jami an tsaro domin tattauna tare da hada Kai domin magance dukkanin kalubale da ake fuskanta a harkokin noma domin bunkasa tare da wadatar da abinci a fadin jahar. Mrs Heidi Sunday ta kirayi masu sayar da kayakin amfanin noma da su tabbata sun Samu takardan izinin sayar da kayakin su daga hu...